HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KATSINA BATA DA ALAKA DA LABARIN DA DCL HAUSA TA WALLAFA
- Katsina City News
- 05 Jun, 2024
- 660
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina bata da alaka da labarin da shafin yanar gizo na DCL Hausa ya wallafa cewa: "Akwai gurbatattun 'Yan jarida da aka ba wa kwangilar lalata Hisbah a jihar Katsina." Wannan labarin ba daga kwamandan Hukumar Hisbah yake ba. Hukumar Hisbah bata yi wata hira da manema labarai ba, kuma wannan kafa ta yanar gizo ta fadi son zuciyarta. Hukumar Hisbah bata san inda kafar DCL ta samo wannan labari ba.
Gwamnatin jihar Katsina ta kafa Hukumar Hisbah bisa tsari da kuma kare dokokin addinin Musulunci (Umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna). Don haka duk zancen da zamuyi muna duba maslahar al'umma da kuma abin da Allah da Manzo suka ce.
A tsawon watanni, Hukumar Hisbah bata kira wani taron manema labarai ba, balle har ta fadi wata magana ta bata suna ga wasu ba. Haka kuma hukumar tana jan hankalin al'umma da su kansu masu kokarin batawa hukumar suna da suji tsoron Allah, su sani cewa "Duk abin da ka fada ko ka rubuta a kan wani gaskiya ko karya, Allah zai tambaye ka ranar Ƙiyama cewa ina ka ji ko ka gani?"
Haka kuma Hukumar ba zata lamunci bata suna ga masu bata mata suna ba, don haka hukumar take kira da a kiyaye.
Babban aikin Hukumar Hisbah a jihar Katsina shine yaki da barna, sanya ɗa'a da gyaran tarbiyya. Kullum hukumar tana samun gagarumar nasara.
Sa hannu:
Malam Nafi'u Ma'azu Akilu,
A madadin Hukumar Hisbah ta jihar Katsina, 05/6/2024