"PDP a jihar Katsina guda ɗaya ce, wanda ya nemi rabata Sheɗan ne" Inji Sanata Tsauri

top-news

Muhammad Ahamed, Katsina Times

A taron da ta kira na bayyana hadin kai ga 'ya'yanta. Jam'iyyar PDP a jihar Katsina bisa jagorancin Sanata Umar Ibrahim Tsauri, Ahamed Rufa'i Safana, Tsohon Sakataren gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Inuwa, Sanata Ahamed Babba Kaita da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina Alhaji Salisu Lawal Uli. Sun bayyana cewa jam'iyyar PDP tanan Daram kuma guda daya ce ba biyu ba, duk wanda yake son maida ita biyu to shedan ne.

A madadin jagororin jam'iyyar ta PDP, sanata tsauri ba yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar da a duba matsalolin da suke haddasa faduwa zabe, don a guarasu.

Tsauri yace "ita PDP ta taka matsayin da babu wata jam'iyya a Najeriya da ta taba kaiwa, amma yau an wayi gari a wasu jihohi PDP tana zuwa na Uku da kyar" yace mi ya ya jawo haka .. ?

A karshe tsauri ya ja hankalin 'ya'yan jam'iyyar PDP na hakika akan hadin kai gyara matsaloli don a gudu tare a tsira tare.

"Kowa yaje yayi tsari tun daga matakin yanki zuwa na ƙaramar hukuma, mu shirya Tunkarar zabe muga ya za a iya kada mu" sakon Honorable Salisu Lawal Uli ga jagororin jam'iyyar PDP na yankin Katsina, a taron wanda aka kasa Shiyya uku kuma ya guda a lokaci daya, daga Karamar hukumar Katsina, Daura da Funtua.

Honorable Uli ya bayyana cewa mutanen da suka tara, sune jam'iyyar PDP kuma idan suka hada kai, zasu cimma Nasara.

Taron na kara bayyana hadin kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyya ya gudana a ofishin Dakta Mustapha Inuwa a ranar Lahadi 26 ga watan Mayu, duk a cikin shirin Tunkarar zaben kananan hukumomi a jihar Katsina.