Bayani akan sabowar dokar Masarautar Kano wanda take jiran karatu na karshe yau da kuma sahalewar Gwabna.
- Katsina City News
- 23 May, 2024
- 531
Daga Sadeeq Sheshe
@ Katsina Times
1- Sabowar dokar ta rushe dokar da Ganduje yayi na shekara 2023 Wato Kano emirate law 2023.
2-Dokar ta rushe Majalisar Masarautar Kano Wato Kano council of chiefs
3-Dokar ta rushe dukkan sarakuna 5 da dokar Ganduje ta kafa har da sarkin cikin gari
4-Dokar ta wargaza Duk nade naden da akayi tun daga lokacin da aka fara kafa dokar a December 2019 zuwa yau. Ma’ana dai Duk wasu nade nade da ciyarwa Gaba da akayi a koina a harkar sarauta a jihar Kano wanda hukuma take sahalewa ya tashi daga aiki
5-Dokar ta bada damar koma tsarin da ake kai kafin December 2019.
6- Da zarar Gwabnan Kano ya sa hannu a wannan doka, To babu sarki a Kano kenan sai wanda Gwabnati ta ayyana sannan ta tabbatar masa ta hanyar bada sabuwar takardar nadi(Wato appointment letter).
7- A wannan kadami, Duk wani sarki wanda dokar Ganduje ta kafa shi, ya koma matsayinsa na Hakimi a da. Misali Sarkin Cikin Birni zai koma Wamban Kano hakimin birni, mukamin da yake kai kafin December 2019.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com