KOFAR SORO: Asalin Unguwar Cikin gida

top-news

UNGUWAR CIKIN GIDA. 

Unguwar cikin gida tana a tsakiyar Birnin Katsina. Tarihin kafuwar wannan Unguwa Yana da nasaba da Gidan Sarkin Katsina Muhammadu Korau, Wanda aka Gina a shekarar 1348. Lokacin da Korau  ya anshi lokaci  daga hannun DURBAWA, Sai ya kawo tsari na Sarauta,  da shugabanchi. Daga cikin irin wannan tsarinne aka samu Sarautu irinsu Shamaki, Magayaki, Shantali, Turaki da sauransu. Mafi yawan Sarautun ana bukatar sune a kusa da Sarki, wannan Yana daya  daga dalilan kafuwar Unguwar cikin gida. Domin zaman da wadannan mutanen Fadar sukayi ya jawo samuwar shiyyoyi da dama daga   harabar Gidan Korau, misali akwai  shiyyoyi irinsu Unguwar Gadi. Unguwar Gadi ta   dade da kafuwa a cikin gida, domin tun Habe har zuwa Dallazawa akwai mutanen da suka zauna a wurin, misali a lokacin mulkin Dallazawa Tarno Abdullahi Barka ya zauna a Unguwar Gadi ta cikin Gida, dalilin kiranta Unguwar Gadi shine zaman da Alin Gadi yayi a Unguwar, Alin Gadi mutumin Kasar Mani Kuma Yaran Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne, tun ma Sarki Dikkon Yana Durbi, lokacin da Sarki Dikko ya zama Sarki ya dauko Alin Gadi daga Kasar Mani ya maido shi cikin gida Kuma ya bashi gida a dai dai inda Unguwar Gadi take, Sai mutane suka rika cema wurin Unguwar Alin Gadi, daga baya aka takaita zuwa Unguwar Gadi. Akwai Kuma shiyyar Garjagau. Ita Kuma Garjagau  tana daya daga cikin Unguwannin cikin gida, Garjagau Badawa suka kafata daliin  zuwan Turaki Agawa, shugaban Badawan cikin gida a lokacin Sarkin Katsina Muhammad Bello wajen shekarsr 1861. Akwai shiyyar Unguwar Kuka, wadda anan Kuma akwai Gidan Sarkin Gandu, da Ajiya da sauransu. Akwai shiyyar Tsamiya anan Kuma shiyyar nan Gidan Sarkin Bindiga yake da Gidan Yari Ammani, sannan Kuma akwai Makabartar Sarakunan Musulunci ta Dallazawa, wadda anan ne aka rufe Malam Ummarun Dallaje, da wasu Sarakuna na Dallazawa, da Galadiman Katsina Dudi. Akwai Kuma  shiyyar Tabkin Lambu, shi wannan Lambun Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944). Anan Tabkin lambunne  Kabarin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, da Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo da Sarki Kabir suke. Akwai Kuma Lungun Makama. Shi Kuma Lungun Makama ananne Makama yake, aikinsa shine ya Kama Mai laifi ya tsare shi, kamin a gudanar dashi gaban Alkali domin yi Mashi Sharia. Akwai Kuma Gidan Korau, duk a cikin gida Wanda Sarkin Katsina Muhammadu Korau ya Gina a shekarar 1348. Shi Gidan Korau Yana a tsakiya, Kuma dukkan wadannan shiyyoyin an zagaye sune da Katanga( Ganuwa)  Kuma akayi masu Kofofi biyu watau Kofar soro da Kofar Bai, Kofar soro itace Kofar shiga cikin gida, ita Kuma Kofar Bai tana a baan Gidan Korau. 

    Abubuwan Tarihi na Unguwar cikin gida sun hada da 1. Kyauren Gobir, Wanda Katsina suka  ciro daga Birnin Alkalawa bayan cinsu da Yaki, 2. Haka Kuma akwai kayan nadin Sarautar Sabon Sarkin Katsina kamar Takobi Gajere, wadda Sarki Korau ya yanka Sanau, da Takobi Bebe, wadda Katsina ta kwace daga hannun Sarkin Gobir Yakuba bayan cinsu da Yaki a shekarar 1795, akwai Tukunyar karfe ta Korau da sauransu. Akwai  Ginin Baitul Mali  na farko  a Nigeria ta Arewa( First Teasuey) Wanda aka Gina lokacin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Akwai Kuma Kabarin Turaki Agawa Wanda yake kallon Gidan Sarkin Katsina. Akwai Dakin Kwaf, Wanda aka budeshi lokacin Sarki Dikko  da sauransu. 

Musa Gambo Kofar soro.

NNPC Advert