Kungiyar APC Akida Forum, ta Buƙaci EFCC ta binciki Ministan tsaro, Bello Matawalle
- Katsina City News
- 04 May, 2024
- 768
Kungiyar APC Akida Forum, ta yi kira ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da ta binciki tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, kuma Ministan Tsaro na yanzu, Bello Mohammed Matawalle, kan zargin almundahana da dukiyar al’umma. jimillar Naira biliyan 70.
A wata takardar korafi da ta mika wa hedikwatar EFCC a Jiya Juma’a, 3 ga watan Mayu, 2024, kungiyar ta bukaci hukumar da ta sake bude bincike kan almundahana da Matawalle ya yi a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara.
A cewar shugaban kungiyar, Malam Musa Mahmud, a baya hukumar EFCC ta binciki Matawalle a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa, bayar da kwangiloli, da karkatar da sama da Naira biliyan 70, amma ana zargin an karkatar da lamarin a karkashin kafet. Inda aka rufe shi nan take.
Kungiyar dai na neman hukumar EFCC ta sake duba lamarin, ta kuma gurfanar da Matawalle a gaban kuliya, bisa la’akari da jajircewar Gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa da kuma bukatar da ta dace wajen hukunta jami’an Gwamnati a kan abin da suka aikata.
Ana zargin Matawalle da karkatar da kudaden da aka tanada domin gudanar da ayyuka a jihar Zamfara da kuma amfani da su wajen biyan kudirinsa na siyasa da dai sauran zarge-zarge.
Kiran na APC Akida Forum na gudanar da bincike ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke daukar kwararan matakai na yaki da cin hanci da rashawa, kuma kungiyar ta bukaci hukumar EFCC da ta nuna aniyar ta na yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar bincike tare da gurfanar da Matawalle gaban kotu idan aka same shi da laifi.