Gamayyar kungiyoyin Makarantun Allo (Tsangayu) na jihar Katsina sun yi kira ga Gwamnati ta waiwaye su.

top-news


A ranar Alhamis 2 ga watan Mayu gamayyar kungiyoyin Tsangayu na jihar Katsina sun kira wani zama na musamman domin kara tabbatar da hadin kansu, gami da kira ga gwamnatin jihar Katsina akan halin da suke ciki na bukatar Tallafawa Almajirci a jihar Katsina.

Gamayyar kungiyoyin kimanin hamsin 50 sunyi zama na musamman ne a zawiyyar Alaramma Malam Sanusi dake Sabuwar Unguwa kwanar Sabis, bisa jagorancin shugaban kungiyar Modern Tsangaya Malam Dahiru Tijjani Filin bugu Katsina.

Taron wanda ya hadu wakilan kungiyoyin daga Daura, Funtua da Katsina sun bayyana hali da irin bukatuwar su ga gwamnatin Dikko Radda akan ya duba tsarin koyarwar makarantar Allo, don bada tallafi ga makaranta Alqur'ani da samar da yanayi mai kyau ga Almajirci da Almajirai.

Alaramma Dahiru Tijjani Filin bugu ya bayyana dalla-dalla akan makasudin zaman da kuma rokonsu ga gwamnatin jihar Katsina.

Shima shugaban Wata kungiya ta samar da koyarwa mai kyau a harkar Almajirai Alaramma Malam Masa'udu ya bayyana cewa, "Mu ba bukatar mu gwamnati ta dibi kudi ta bamu b duk abinda za a bamu kafin shi muna rayuwa, bukatar mu shine Almajirai, ina zasu rayu, ina zasu kwanta mi zasu ci..?. Don haka yace anan kiransa ga mutum uku ne, na farko Iyayen yara masu kawo 'Ya'yansu makarantar Allo, su ji tsoron Allah su kawo 'Ya'yansu da abinda zasu ci. Na biyu ga makamai su dubi Allah su kawo tsari da zai taimaki Almajiran da kuma kin yarda su amshi yara madamar basu da wajen kwana mai kyau, kuma uba bai hado dansa da abinci ba. Yace kira na uku, gwamnatin jihar Katsina ta taimaka ta samar da wuraren da Almajirai zasu iya rayuwa kamar dan kowa, duba da abinda suke karantawa. Yace inda ake bukatar ruwa, a samar da ruwa, inda ake bukatar wurin kwana gwamnati ta samar da shi dama wasu abubuwa na more rayuwa. A karshe yayi kira ga masu hannu da shuni suma su taimaka.

Gwanaye da Alarammomi da suka samu halartar da tofa albarkacin bakinsu sun hada Alaramma Muktar Aliyu, Mal. Dahiru Ahamed Tijjani, Malam Ahamd Suyudi Adam, Gwani Shehi Malam Sanusi, Malam Balarabe da sauran su.