GWAMNAN ZAMFARA ZAI INGANTA RAYUWAR MA AIKATAN JAHAR
- Katsina City News
- 01 May, 2024
- 646
@ Katsina Times
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa ta inganta rayuwar ma'aikatan jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne wurin gagarumin taron ranar ma'aikata, wanda aka saba gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan a kowace ranar ɗaya ga watan Mayu, wanda na jihar ya gudana a Sakatariyar JB Yakubu Secretariat Complex da ke Gusau a yau Larabar nan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta na nan a kan bakar ta na tafiya tare da ma'aikatan a duk harkokin mulkin jihar.
Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ƙara da cewa, a jawabin Gwamnan ga ma'aikatan, ya yi alƙawarin aiwatar da tsare-tsaren sa guda shida da ya tsara don haƙƙaƙa shirin nasa masa na tsamo jijar Zamfara daga halin da ya same ta.
“Gwamnatina ta yi na'am da muhimmiyar rawar da ma’aikata ke takawa wajen ƙaddamar da ayyuka da aiwatar da manufofin gwamnati. Ma'aikata da gwamnatoci abokan haɗin gwiwa ne wajen aiwatar da ayyukan ci gaban al'ummarmu.
“Ma’aikata ne ke taimaka wa gwamnati wajen cimma burinta na samar da ayyuka ga jama’a. Bisa la’akari da haka, za mu ci gaba da lalubo hanyoyin inganta jin daɗin ku da na iyalanku, musamman idan aka yi la’akari da irin matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur da manufofin kuɗi da ya haifar da koma-baya a darajar Naira da hauhawar farashin kayayyaki da ba a taɓa ganin irinsa ba a ƙasar nan.”
Gwamnan ya kuma bayyana wasu nasarorin da gwamnatin sa ta samu a cikin watanni goma sha ɗaya na farko a kan karagar mulki.
“Ya ku ’yan uwana, ina mai farin cikin bayyana cewa a cikin watanni goma sha ɗaya da kafa gwamnatinmu, ma’aikata a Jihar Zamfara suna jin daɗi. Mun fara ta hanyar kawar da giɓin albashin da muka gada tare da tabbatar da biyan albashin akan lokaci, tare da tsawaita wasu abubuwan jin daɗin rayuwar ma'aikata.
“Don ci gaba da wannan yunƙuri, gwamnati ta aiwatar da hanyoyin da za a tabbatar da cewa ma’aikata na gaske ne kaɗai ke cin gajiyar albashinmu. Har ila yau, muna tuntuɓar ma’aikata kan batun albashi, bisa la’akari da yadda rayuwa ta ke a yau. Ina yaba wa da goyon bayan da gwamnatina ke bayarwa da kuma dangantakar da ke tsakaninta da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a jihar. Haƙiƙa yana ɗaya daga cikin nasarorin da ake samu na ci gaba wajen maido da inganta harkokin gwamnati.
Bugu da ƙari, gwamnan jihar Zamfara ya yi alƙawarin daidaita dukkan ayyukan gwamnati da kuma gyara ayyukan ma’aikatan gwamnati domin ɗaukar salon gudanar da harkokin gwamnati na zamani.
“Don inganta harkokin gwamnati, nan ba da jimawa ba za mu bayyana tsare-tsaren mu na zamanantar da duk ayyukan gwamnati da kuma sake fasalin ma’aikatan, don aiwatar da tsarin tafiyar da harkokin gwamnati na zamani.
"Wannan zai haɗa da sabbin hanyoyin tantance ayyukan ma'aikata, horarwa da tabbatar da ƙwarewarsu a tsakanin wasu tsare-tsare da dama.
“Hakazalika, gwamnati ta ƙuduri aniyar hana zamba da wasu munanan ɗabi'un da suke gurɓata ayyukan gwamnati.
“Saboda sadaukarwar da ma’aikata suka yi a lokacin hidimarsu, ya dace a riƙa girmama su da mutunta su. Wannan ne ya sa muka ɗauki matakin biyan bashin garatuti da gwamnatinmu ta gada. Da zarar mun kawar da basukan, za mu tabbatar da biyan duk waɗanda suka yi ritaya daga ayyukan gwamnati da na ƙananan hukumomi cikin gaggawa.
"Da wannan aiki, In Sha Allahu, ma’aikata ba za su sake samun wani dalilin da zai sa su ji shakkar yin ritaya ba, wanda yakan haifar da kwaɗayin ci gaba da aiki.