Tatsuniya: (12) Labarin Kishiyoyi biyu.

top-news

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wasu kishiyoyi biyu masu zaman lafiya a tsakaninsu a wani gari Ba su taba 6ata wa juna rai ba. Suna nan, sai wata rana daya daga cikinsu ta kwanta jinya. To da ma kowaccensu tana da 'ya mace, 'ya' yan kuma sun yi kama da juna ainun, yadda ba kowa ne zai iya bambance su ba, tamkar dai 'yan biyu.

Da mai jinyar nan ta ga alamun ciwon nata ba na tashi ba ne. sai ta kira kishiyarta, ta ba ta amanar 'yarta. Kishiyar ta karba, kuma ta yi alkawari za ta kula da duka yaran biyu kamar ita ta haife su.

Da mai jinyar ta rasu, sai kishiyar ta ci gaba da kula da yaran har suka girma, suka zama ' yan mata. To amma saboda tsabar so da adalci da take yi wa 'yar kishiyarta, sai ya zamanto ba ta iya gane 'yarta daga cikinsu, domin kamanninsu daya.

Sai wata tsohuwa ta ziyarce su da ta lura da yanayin matar ta hanyar adalcin da take nunawa a tsakanin yaran, sai ta rinka yi mata fada a kan yaya za ta riki dan wani kamar nata. 

Sannu a hankali, har dai ta fara karkata ga zancen tsohuwa, to amma sai ta ce ba za ta iya gane diyarta daga cikin yaran ba. Sai tsohuwar nan ta ba ta shawara da cewa in sun je daukar ruwa kafin su dawo, ta dafa dambu, ta ajiye a bakin randa, in sun dawo suna jin yunwa za su fara ci.

To sai ta bari sai sun fara cin dambun sai ta daka musu tsawa, tana cewa: "Kun san yadda yake ne, ba ku tambaya kafin ku fara ci?" Tsohuwa ta ce mata ta lura da kyau, domin wadda ta fara cire hannunta daga akushin dambun to ita ce 'yar kishiyarta. 

Wadda ta ki cire hannunta kuma ta ce suna jin yunwa ne, to ita ce 'yar cikinta.

Sai kuwa matar nan ta yi hakan, ruwa sai suka hangi dambu a bakin randa, suka nufi bakin randa da gudu. suka fara cin dambu. Nan take sai ta daka musu tsawa, tana cewa: 

"Kun san vadda dambun yake ne, ba ku tambaya ba kafin ku fara ci Bayan yaran sun dawo daga daukar Nan da nan suka razana, sai 'yar kishiyarrta ta cire hannunta daga cikin akushin dambu, ita kuma 'yarta ta cikinta, muna jin yunwa ne fa.

ta yi mata tsaga a fuska. Daga nan sai ta kama 'yarta ta kai daki, kuma ta dubi uwar ta ce: karbi abinci. Haba mama,
Daga nan fa sai ta fara gana wa 'yar kishiyar nan tata azaba iri-iri, ba ya kai ga in za su ci abinci, sai ta kii zuba wa 'yar kishiyarta nata abincin a ta kama 'yar kishiyarta akushi, sai ta zuba mata a kasa. Amma kuma maimakon 'yar kishivar nan rame ko ta damu, sai kiba kurum take yi. 

Daga nan sai ta daina ba ta ahin sam-sam, har ma dai ta kore ta daga gidan, wai ta je can kabarin uwarta ta Da yarinya ta ji haka, sai ta yi ta kuka, ta kama hanya ta tafi bakin kabarin uwarta tana kuka.

Ana haka, ana haka, wata rana da ta je kabarin uwar tana kuka, sai uwar ta fito ta rarrashe ta, ta ba ta abinci, ta ci ta koshi. Haka dai, kullum sai ta je bakin kabarin uwarta, ta fito ta ba ta abinci.

Nan da nan ta sake yin kiba, ta yi kuma kyau, ta goge, abin gwanin ban sha'awa Ita kuwa mai uwa a murhun, sai ramewa take yi. Uwarta ta rasa abin da za ta yi.
ki ci, ta ci gaba da tafiya. Wata rana sai wasu samari suka je tambayar uwar cewa daya daga Cikinsu yana son ya shiga neman auren marainiyar.

Maimakon ta yi abin da samarin suka nema, sai ta ce sai dai su auri 'yarta. Su kuma suka ce waccan mai tsaga a fuska suke so. Amma sai ta hana su, ta mna kore su, ta gaya musu kada su sake zuwa gidan neman aure in ba 'yarta suke so ba.

Da marainiyar nan ta ga haka, sai ta gudu, ta shiga uwa duniya. Ianu cikin tafiya a dokar daji, sai ta ga shinkafa da nama. Sai shinkata ta yi Wa budurwar nan magana, ta ce idan tana iin yunwa ta zauna ta ci. Amma sa yarinya ta ce ta koshi, kuma ta ci gaba da tafiya.

Can kuma sai ta ga naman kaza, sai naman ya yi mata tayi, amma sai ta
Haka ta rinka haduwa da kayan dadi iri-iri, amma ta ki amsa tays hakura da yunwar da take ji, ga bakin cikin da ke damun ta.

Tana cikin tafiya sai ta ga hadari ya hadu. ita kuma babu inda za fake. Ta duba nan, ta duba can, sai ta hangi wata'yar bukka, nan take ta: ta a guje, ta bude ta shiga. Bayan ta zauna sai ta ga wani babban kumurcia getenta. Sai macijin nan ya sulalo ya nufo wurinta, amma ba ta ji tsoro sai kallon sa take yi.

Tana cikin haka da macijın nan, sai wani karamin yaro ya bullo dauke da kayan abinci, ya gaya mata ta ba macıjin nan abinci. Nan da nan ta ba shi mIwa va sha, kumna ta ba shi abinci ya ci. Da ya koshi sai ya rufe baki.

Bavan ta kammala ciyar da macijin nan da shayar da shi ruwa, sai yaron va tambaye ta ko ita ma za ta ci abincin ne, Sai ta ce ta koshi. Sai macijin nan ya sake yin kokarin razana ta, amma sai ta ce ita komai a 0a dama ya yi mata, domin ba ta da wurin zuwa, kuma ta riga ta sadaukar da rayuwarta.

Da in haka, sai nacijin ya shiga rikida, yana zama namun daji daban-daban, amma duk da haka ba ta razana ba. Maimakon haka ma, sai ta gvara tona kallon ikon Allah, har dai macijn nan ya rikida, ya koma yaro matashi kyakkyawa.

Yarinyar ba ta sani ba, ashe macijin nan dan Sarki ne yake neman aure. amma sai ya bi wannan hanya don ya sami mace mai hankali, mai amana. Nan da nan ya sa aka dauke ta a kan doki, aka kai ta gidan Sarki, aka đaura mata aure da shi, aka sha biki.

Bayan an gama biki sai aka tura yaro ya gaya wa amarya za a zo a yi mata kitso, to amma matar da za ta yi mata kitson mayya ce, kuma za ta zo da kayan ciye-ciye a hannunta, idan ta ba ta kada ta ci. Yaron ya ce mata ta rike duk abin da za ta ba ta a hannunta, ko sau nawa ta ba ta kuwa kada ta sa a baki. Yaro ya kara bayyana mata cewa, bayan wannan mayya ta gama kitso za ta yar da matsefata a gidan, amma kada ta gaya mata, ta kyale ta ta tafi. Bayan ta tafi kuma za ta dawo ta tambayi matsefatar, to sai ta mika mata hade da kayan ciye-ciyen da ta ba ta.

Amaryar ta amince. Da makitsiya ta zo gidan, sai aka ce ta je ta yi wa amarya kitso. Da ta fara kitso sai ta mika wa amarya kayan kwalama, wai ta dan lashe bakinta da shi, sai amarya ta karba kamar za ta ci, amma sai ta rike a hannunta. Jim kadan kuma sai ta sake mika mata wani abincin, sai amarya ta karba ta hada sua hannunta. 

Haka dai har sai da suka gama kitso,
nakitsiyar ta tashi za ta tafi. sai ta var da matsefin da ke hannunta a tsakar dakin amarya, amma amarya ta ki gaya matad. Makitsiya ta kada kai ta yi tafiyarta. 

Bayan wasu 'yan sa'o'ida tafiyarta al ta dawo, wai ta manta matsefinta a gidan, sai amarya ta dauko mata, ta hada mata da kyautar da ta ba ta ta kavan kwalama a lokacin da take yi mata
kitson.

Da mayyar nan ta ga an dawo mata da tarkacenta, sai kawai ta fara zage- age, ta kama hanya a fusace ta fita abinta. Amarya da mijinta dan Sarki suKa ci gaba da zamansu cikin in dadi, Wata rana sai amarya ta kwanta a daki ita kadai tana ta rusar kuka. 

Da mijinta ya shigo sai ya tambaye ta abın da ya a faru, sai ta ce tana tunanin gidansu ne da mahaifinta da kuma kishiyar hanaifiyarta wadda ta rike ta. Ta kwashe labarinta gaba daya ta gaya masa.

Da ya ji bayaninta, sai ya tambaye ta tana iya gane garin, sai ta ce ta sani. Ba tare da bata wani lokaci ba, sai ya ce ta shirya su je su kai musu ziyara. Jin haka ya sa ta shiga murna da shirye-shiryen tafiya. Ta tanadi kayan sutura da sauran kayan masarufi.

Da ranar da suka sa ta zo, sai Sarki ya sa aka hada su da dawakai da 'yan rakiya masu yawa, sai ka ce ita ce matar Sarki, suka kama bm Da suka isa garin, sai ita da mijinta da 'yan rakiyarsu suka nufi gidan ivayenta, suka shiga gidan, mutanen garı kuma suna ta mamakin vadd wannan yarinyar da aka ba wuya a baya ta koma.

Da 'yar'uwarta ta gan ta sai ta rungume ta, amma da kishiyar uwarta ta fito sai ta ce ba ita ce ta bata ba, to amma saboda tsagun fuska da ta yi mata sai ta gane ta. Nan take suka rungume juna cikin murna.

Bayan amarya ta huta sai suka fara hira, ta kwashe labari tun daca barinta gida har zuwa lokacin da ta auri dan Sarki. Da ta gama ganin danoi sai ita da mijinta suka yi musu sallama, suka kama hanya tare da'ya rakiyarsu, sai garin mijin.

Bayan tafiyarta sai kishiyar uwarta ta ce lallai ita ma 'yarta ta je ta auro đan Sarki. A kan dole yarinya ta amsa. Da ta kama hanyar tafiyar neman dan Sarkin da za ta aura, kamar dai yadda 'yar'uwarta ta yi, tana shiga daji sai ta ga shinkafa da nama.

Tun kafin ma a yi mata magana sai ta tsuguna ta fara ci. Sai shinkafa ta ce da ita:

Yan mnata zo ki ci shinkafa. Da budurwa ta ji haka sai ta dubi shinkafa ta mayar mata da jawabi: "Da ma ko ba ki yi magana ba, ai ina jin yunwa. Sai ta ci gaba da cin shinkafa har ta koshi. Daga nan sai ta kama hanya ta fara tafiya. Ba ta yi nisa ba kuma sai ta hadu da naman kaza. Nan ma ta zauna ta ci har ta đebi cinya da fukafukai da Rirjin kaza a hannunta, ta y1
guzuri.

Ta sa kai ta fara ci gaba da tafiya tana lasar baki. Ba jimawa sai hadari ya taso, ta rasa yadda za ta vi. Ga shi ba garni kusa a baya, kuma ba ta san inda ta dosa ba. Can sai ta hangi wata 'yar bukka, t ruga a guje ta shiga, sai ta ga wani shirgegen maciji. 

Tana ganin macjn han sai ta kwala ihu, tana neman hanyar gudu. Sai dan yaro ya bullo dauke da abinci, va ce ta ba macijin abinct. Sai ta ce:Tabdi! Ta yaya ina jin yunwa in ga abinci in ba wani
maciji? Sai ta kama cin abinci, ta yi watsi da maciii. lim kadan sai macijun ya
fara rikida. Tana ganin haka sai ta fadi sumammiva, watau ba ta ga Sarki ba, balle ta san kamanninsa. 

Bavan ta farka sai ta gan ta a gidan Wase masu sarauta, anmma talakawa ne da wani dan yaro ya zo ya gaya mata cewa za a zo a yi mata kitso, amma idan makitsiyar ta ba ta abin kwalama kada ta ci.

Tana jin wannan ka'ida sai ta ce: *Tabdi! Ai ni in har na ga abin dadi ba zan kyale shi ba sai na ci" Da makitsiya ta zo ta fara kitso sai ta mika wa yarinyar abin kwalama, sai ta karba ta kai baki ta cinye. 

Da ta sake mika mata na biyu sai ta sake lankwamewa. Bayan sun gama kitso sai makitsiyar ta yar da matsefinta, sai ta ce da ita: "Ai kin manta matsefinki."

Sai ta juya ta karba, ta tafi tana dariya. Bayan wasu 'yan kwanaki sai yarinyar nan, abin tsautsayi ta kamu da cuta, wadda ta zama ajalinta aka binne ta, ba tare da ta auri dan sarkin ba. 

Kurunkus.

Munciro daga cikin littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman