Ziyarar Gwamna Dikko Radda kasar Holland ta haifar da Ɗa mai ido -Isah Miqdad
- Katsina City News
- 23 Apr, 2024
- 534
A ranar 18 ga watan Fabrairun 2024 ne Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya jagoranchi tawagar shugabannin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Katsina zuwa wata ziyarar aiki a kasar Neitherlands wadda aka fi sani da Holland domin ganawa da masana akan harkar ruwa domin kawo dauki ga jihar Katsina wajen magance matsalar ruwa a jihar.
A lokacin ziyarar aikin, gwamnatin Johar Katsina ta gana da babban kamfanin CFM wanda ya shahara akan harkokin ruwa a fadin duniya baki daya, inda aka tattauna muhimman al’amura da suka hada da ingantattun hanyoyin samar da ruwan sha da kuma zuba hannun jari a harkar ruwan sha a Jihar Katsina.
A bisa ga wannan tattauna da gwamnatin Jihar Katsina tayi da wannan babban kamfani na Kasar Holland, a jiya ne, ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu 2024, jami’an Kamfanin CFM dake Kasar Holland da kuma jami’an Kamfanin InfraCo Nigeria suka iso jihar Katsina domin gudanar da binciken kwakwaf da kuma gane ma idon su irin jarin da gwamnatin jihar Katsina ta zuba a harkar ruwan sha a Jihar.
Mai Girma Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Hamza Sulaiman Faskari, da Injiniya Tukur Tinglin da Babban Dan Kwangila Alh. Salisu Mamman suka tarbe su a filin jirgin sama dake Katsina.
Shugaban Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Katsina, Injiniya Tukur Hassan Tingilin, shine ya jagoranci tawagar zuwa aikin gani da ido a babban dam dake Ajiwa tare da ziyarar inda ake tacewa da tsaftace ruwan kafin ya isa zuwa ga al’umma.
Muhammad Abdullahi Kaita wanda shine shuganan dam Ajiwa yayi bayani irin yadda ake gudanar da wannan aikace aikace da irin yadda gwamnatocin da suka wuce suka bada gudummuwar tun kafuwar wannan waje wanda ya shafe tsawon shekara kusan hamsin da ginawa sannan yace ita wannan gwamnatin ta Mal Dikko Umar Radda tabada muhimmiyar kulawa domin inganta dam din.
Daga Ajiwa, tawagar ta ziyarci tashar ruwa ta kofar kaura, Fatima shema, da Tayoyi bayan kammala ziyarar shugaban tawagar bakin, Mr Achi, ya bayyana gamsuwar shi da irin yadda ya ganema idon shi irin kayyayakin da aka sanya domin samar da tsabtataccen ruwan sha a Katsina.
Tawagar ta rufe da ziyara zuwa ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina a fadar gidan gwamnatin jihar.
Wannan ziyara da Kamfanin CFM da InfraCo suka kawo a jihar Katsina na da nufin duba irin shirin da gwamnati tayi a kan harkokin albarkatun ruwa domin juba jari don inganta ruwan sha a Jihar Katsina. Wannan hadin gwiwa da gwamnatin Jihar Katsina zata yi da wannan manyan kamfanonin zai inganta samar da ruwan sha zuwa Kananan Hukumomi sama da Ashirin da Biyu (2) a fadin Jihar Katsina.