An cigaba da sayar da Manfetur a gidajen Man AJASCO a rassan shi dake jihar Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

An ci-gaba da bada mai kamar yanda aka saba a gidajen Man Kamfanin AJASCO bayan da Gwamnatin jihar Katsina da bada Umarnin bude shi.

A ranar Laraba 18 ga watan Afrilu ne Kwamitin Kula da hauhawar farashin kayan Abinci da Gwamnatin jihar Katsina tá kafa ta bada Umarnin bude gidajen man guda uku, "AJASCO" da wasu guda biyu bayan rufe su da kwamin yayi a bisa zargin saida man da ya sabawa ka'ida.

Kwamitin a karkashin jagoranci Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Katsina Alhaji Jabiru tsauri ya jagoranci wani rangadi a birnin Katsina domin nemowa da gano yanda ake boye abinci ko sayar da shi da tsada, inda sukai dirar mikiya a gidan man AJASCO, Mai Mammada, da Mamasco, wanda suka garkame gidajen man domin gudanar da bincike.

A ranar Laraba: bayan gudanar da bincike kwamitin ya wanke dukkanin Kamfanonin Man tare da basu damar cigaba da saida Mansu kamar yanda aka saba.