Tatsuniya (3): Labarin Kura da Zomanya...
- Katsina City News
- 06 Apr, 2024
- 781
Ga ta nan, ga ta nanku.
A can cikin wani kungurmin daji akwai wata Zomanya mai cikí, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na makwabta.
Wata rana sai Zomanyar nan ta je wurin Kura ta ce mata: "Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rínka boye
'ya'yanmu. Sai Kura ta ce: E, gaskiya ne, to amma bari mu tona rami babba domin mu saka 'ya'yanmu a ciki." Da suka tona rami sai suka zauna tare, har lokacin haihuwarsu ya yi.
Da suka haihu, sai suka tara 'ya'yansu a rami daya, kuma suka yi alkawari cewa Kura za ta rinka samo musu abinci, ita kuma Zomanya za ta rinka renon 'ya'yansu. Suka zauna, in Kura ta tafi neman abinci ta dawo, sai ta mika wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ya'yansu. Kullum haka.
Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo mata abinci sai ta ba 'ya'yanta su ci, in sun koshi sai ta cinye sauran, ta hana 'ya'yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar 'ya'yanta sai Zomanya ta ce ai sun ci abinci sun koshi, suna barci. Haka suka yi ta yi, har dai wata rana Kura ta ce saí ta ga 'ya'yanta. Da ta leka ramin ta jawo 'ya'yanta sai ta ga duk sun rame. Sai ta tambayi 'ya'yanta abin da ya same su, suka rame haka.
Sai 'ya'yan suka ce ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta hana su, ta bai wa 'ya'yanta, su kuwa sai ta sa su yi barcin dole kullum.
Da jin haka sai ran Kura ya baci, ta yi kuka, ta yi gurnani da karaji mai tsanani, ta ce tun da Zomanya ta ci amanarta, to ita da 'ya'yanta za su cinye Zomanya da 'ya'yanta gaba daya.
Ko da Zomanya ta ji abin da Kura ta fada, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka raina fata.
Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta ce: "To shi ke nan, tun da kin ce ni da `ya'yana mun zama nama, to ki yi hakuri mu fito daga rami tukuna.
Zomanya ta shiga rami ta gaya wa 'ya'yanta idan ta fita Kura ta bí ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura ta sake magana, sai Zomanya ta hada manyan kunnuwanta biyu, ta dan miko su waje ta ce da Kura: "Don Allah ki rike mini takalmana kafin in fito."
Jin haka sai ya sa ran Kura ya baci, ita a tsammaninta yaya za a yi kamar Zomanya ta ce ta rike mata takalmanta, bayan ta zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da karfi ta finciko su ta jefar, wai ita a nufinta takalma ne.
Sai kunnuwa suka sullube, Zomanya da 'ya'yanta suka ranta a na kare. Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko daya daga cikinsu.
Da ba domin Gizo ba da na shara muku karya.
Kurunkus.
Mun ciro wannan Labarin ne daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman