Tatsuniya (1) Labarin Marainiya

top-news

Marainiya

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wata yarinya marainiya, watau wadda take ba uwa ba uba: kuma ita kadai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulakanci a wurin kishiyar uwarta, wadda take da 'ya'ya maza da mata, wadanda duka suka taru a kanta suka rika yi mata wulakanci.

A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je gindin wata bishiyar kurna ta zauna, ta yi ta kuka. Wannan kurna tana yin 'ya'ya masu yawa, ga kuma zaki zakwai. Abincinta ke nan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta đebo wadanda za ta ci da dare. To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda 'yar
kishiyar uwarta take so, to amma shi kuma ba ya son ta. Shi ma kuma yakan
je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da marainiyar take zama a gindinta, ta sha 'ya'yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi
don ganyen bishiyar ya boye shi.

Shi ke nan, wata rana marainiya tana zaune sai dan sarki ya sauko daga
bishiya sai ya ce: "Sannunki 'yan mata."
Sai ta ce: "Yauvwa samari. Aminu ya ce: "Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la'asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni ba."
"To yaya kake zama a kan bishiyar kurna mai kaya?" Ta tambaye shi.

Sai ya ce: "Ni na san dabarar da nake yi."
Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce: Ni dai marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba." Sai dan sarki Aminu ya ce: "Yau na zama uwa da uba a wurinki." Suna nan yana kiran ta, har ya fara zuwa gidan su marainiya. Da yar kishiyar ta gane dan sarki ne yake zuwa wurinta, sai ta ce ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zO wurin marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba daya alluran suka shiga jikinsa. Nan da nan ya fara jin zazzabi, ya tashi ya tafi gida. Ciwon dan sarki dai ya gagara warkewa, babu
irin maganin da ba a yi ba.

Wata rana marainiya ta tafi diban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar dan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jika masa ya sha to zai warke. Da marainiya ta ji sai ta yi maza ta dauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da bakin tukunya, ta sa kayan maza, ta dauki kwano, kamar almajiri zai je bara.
Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo kashin tsutsa mai
cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa wurin tsutsotsin.

Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lalubowa dai-dai. Bayan ta sami abin da ta je nema, sai ta kama hanyar garinsu, ta isa lafiya. Bayan ta dan huta, sai ta kama hanyar gidan Sarki, ta tarar mutane makil sun cika fada suna jiran mutuwar Aminu. Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun dauka namiji ne, suka ce: "Kai kana ganin dan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don ba ka da kunya?" Sai ta ce:

"Ku bar ni in duba shi ko zai warke. Akwai wani magani da nake tafe da shi." Sai suka daka wa dan almajiri tsawa, suka ce: "Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi sai kai?" Sai ta ce: "A bar ni mana in dan gwada." Da kyar aka bar shi ya shiga. Da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jika, ta ba dan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai. Kowa yana mamakin dan almajiri.
A cikin farin ciki Sarki ya ce: "Zan ba ka gida da dawakai da dukiya mai yawa." Shi ma Sarki bai san da mace yake magana ba.

Sai ta ce: A' a ba na son wannan. Sai Sarki ya ce: To me kake so?" Ba tare da 6ata lokaci ba, marainiyar da ake zato namiji ce ta ce: "Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa. Dan sarki Aminu bai taba zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai

ya cire ya ba ta. Ta karba ta tafi. Bayan kwana biyu sai ya je gidan su marainiya a cikin fushi, ya ce da ita: "A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taba zuwa gani na ba." A cikin tattausar murya ta kalle shi ta ce: "Zauna ka ji labari." Ya zauna ta fara gaya masa yadda ta yi. Da ta gama sai ya ce: "Karva ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa dan almajirin?" Sai ta ce: Zobe."
Ya ce: To idan ke ce, nuna min zoben."
Sai ta dauko ta ba shi. Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya dauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin kome. Ya sa aka daura musu aure, aka yi gagarumin biki, kuma aka ba su kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke.

 Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
*Rabon kwado ba ya hawa sama
*Mai nema yana tare da samu
*Mai rabon ganin badi ko ana ha maza *ha mata sai ya gani.
*Hassada ga mai rabo taki ce.
Mun ciro daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Bukar Usman.