Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Kira ga Malaman Addini Da Su Guji Zage-zage ko cin zarafin Najeriya A Wuraren Wa’azi
- Katsina City News
- 29 Mar, 2024
- 338
Shugaban ya yi kiran ne a wajen taron bude baki da fadar gwamnatin ta shirya wa Malaman Addinai da Sarakunan gargajiya a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.
Shugaban ya jaddada muhimmancin rawar da malaman addini ke takawa wajen samar da hadin kai a tsakanin ‘yan kasa. Ya kuma bukaci shugabannin da su kara zage damtse wajen tona asirin wadanda aka zaba akan mulki da ba su yi abinda ya dace ba.
Shugaban Tinubu ya ce gwamnatin sa ta kuduri aniyar mayar da kalubalen da Najeriya ke fuskanta zuwa nasara ga kasar, ya kuma nanata cewa babu wani dan ta’adda da zai iya kayar da muradu da hadin kan ‘yan Nijeriya, duk yadda suke kokarin cin zarafin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Shugaban ya bukaci sarakunan gargajiya da Malaman addini da su bai wa gwamnati hadin kai domin dakile ayyukan ta’addancin ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane da ma sauran laifuka a kasar nan.
“A jiya a Abuja na halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Okuama, jihar Delta.
Da idona na ga matan su wasu da ciki wasu da goyo, amma mazajensu sun bar su saboda soyayyar kasar nan. Soyayyar kasar nan tana hannunku ku yi wa kasarmu addu'a, Mu tarbiyantar da yaran mu masu tasowa da kishin kasa . Wa’azin da muke yi a masallatai da coci-coci suna da muhimmanci"
“Kada ku la'anci Kasarku. Akwai wani karin maganar Yarbawa da ke cewa, Duk santsin Kugun jinjiri ba za a cire masa jigida ba.
"Wannan ita ce kasarku tilo; kar ku rika Allah wadai da ita a cikin wa'azozinku, kuna iya cewa "Eh, wannan shugaban bai dace da kasarmu ba. Amma ku jira har zuwa zabe na gaba don ku sauya shi, amma kada ku la'anci kasar ku. Kar ku zagi Najeriya. Najeriya kyakkyawar ƙasa ce"
A ci gaba da jawabin, shugaban ya yi godiya bisa taya murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kuma fatan alheri da aka yi masa, ya tunatar da shugabannin cewa ranar haihuwarsa a ranar 29 ga Maris, 2024 ta zo daidai da ranar Juma’a ranar Salla a Musulunci. “Na samu karramawar ranar zagayowar ranar haihuwata a babbar rana, wato Juma’a , ku kuma ina muku fatan komawa gidajenku lafiya a yau Alhamis. Allah ya yi muku jagora Ya kula da ku da iyalan ku, Ya kuma kara rufa mana asiri, Amin"
in ji shugaban kasar.