Cewar Minista Idris Tinubu na kan aikin rage matsalolin Nijeriya
- Katsina City News
- 23 Mar, 2024
- 297
Daga shafin Mujallar FIM
MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri su yi imani da gwamnatin Tinubu.
Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin buɗa baki da ya yi tare da shugabanni da ma'aikatan kafafen yaɗa labarai wanda ma’aikatar ta shirya a ɗakin taro na Armani Events Centre da ke Kano.
Idris ya ce gwamnatin Tinubu tana aiki tuƙuru domin ganin ta shawo kan matsalar tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ya ce, "Ma'aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta himmatu wajen tabbatar da gyaran hukumomin da ke ƙarƙashin ma'aikatar da nufin inganta fannin."
Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin na ƙoƙarin farfaɗo da matatun man fetur na ƙasar nan, inda ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki.
Game da cire tallafin man fetur da aka yi, Idris ya ce Nijeriya ta fuskanci raguwar yawan man da ake amfani da shi a cikin gida na kimanin lita biliyan ɗaya bayan cire tallafin, wanda ya nuna kashi 53 cikin 100 na yawan man da ake amfani da shi da farko.
Ya ƙara da cewa, “Hakan ya bayyana yadda ake safarar man fetur ɗin mu ta kan iyakokin ƙasar nan domin amfanar waɗanda ba sa biyan ƙasar nan haraji”.
Ya jaddada cewa cire tallafin man fetur ya zama dole domin waɗanda ba sa biyan haraji sun fi ‘yan Nijeriya cin gajiyar tallafin.
A cewar sa, “Abin da ake amfani da shi na man fetur a cikin gida ya ragu da kusan kashi 53 cikin 100, ma’ana sama da lita biliyan ɗaya da muke amfani da ita a lokacin cire tallafin ta ƙare a yanzu. Kuma tambayar da za ku yi wa kan ku ita ce: Ina wannan man ya ke zuwa?
“Yaya ba zato ba tsammani amfanin cikin gida ya ragu da kashi 53 cikin 100? Wannan yana nufin cewa wannan man fetur ɗin ya samo hanyar fita daga kan iyakokin mu don amfanin waɗanda ba sa biyan haraji ga ƙasar nan.
“Ba shi da ma’ana a ci gaba da ba wa gidan wani tallafi lokacin da rufin ku ke ɗiga, taga ta karye, kuma yaron ku bai je makaranta ba. Dole ne ku tallafa wa kan ku kafin ku ba wa wani tallafi.”
A kan abin da gwamnati ke yi don rage wahalhalun da ke tattare da cire tallafin, sai ya ce, “Akwai ƙarin albashi na wucin gadi na naira 35,000 a kowane wata na wata shida – an riga an biya na watanni huɗu.
“Gwamnonin Legas, Osun, Oyo, Ogun, Jigawa, Adamawa, Ebonyi, Neja, Ondo da Ekiti su ma sun ɗauki wannan shiri na Gwamnatin Tarayya na biyan albashin ma’aikatan su. An buƙaci sauran gwamnatocin jihohi su aiwatar da irin wannan.
“An kafa Kwamiti Uku kan sabon mafi ƙarancin albashi kuma tuni ya fara aiki. Masu ruwa da tsaki a shiyyar siyasa guda shida su na gabatar da takardar da ke nuna sabon mafi ƙarancin albashi ga gwamnati, ana ci gaba da tattarawa.
“Shugaba Tinubu ya amince da kafa Asusun Tallafawa Ababen More Rayuwa ga Jihohi don su zuba jari a muhimman wurare da za su samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa kuma akwai shirin fitar da motoci masu amfani da gas na naira biliyan 100, don isar da motocin bas masu amfani da gas, da kayan aikin canza motocin.
"Tuni, Shirin Shugaban Ƙasa na Iskar Gas (CNG) ya fara tallafa wa abokan hulɗa masu zaman kan su da na gwamnati a wannan fanni.
“An fara bayar da kuɗi naira 25,000 a kowane wata ga miliyan 15 daga cikin gidaje mafiya talauci da marasa galihu a Nijeriya, wanda aka shirya na tsawon watanni uku. Magidanta 3,140,819 sun riga sun sami biyan kuɗi na farko kafin a dakatar da shirin don dubawa da gyarawa.
“Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a fitar da hatsi tan 42,000 daga Asusun Ajiya na Nijeriya, don raba wa marasa galihu kyauta da Jami'an Tsaron Farin Kaya (DSS) da Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) suka himmatu wajen sa ido a kan rarrabawar.
“Shugaban ya kuma amince da naira biliyan 100 don tallafa wa Asusun Raya Aikin Noma na Ƙasa (NADF) a shekarar 2024 kuma Ma’aikatar ta fara aiwatar da ayyukan fitar da naira biliyan 200, wanda Shugaban Ƙasa ya amince da shi, ta hanyar sababbin kuɗaɗen shiga tsakani na musamman guda uku wanda aka kafa a matsayin wani ɓangare na matakan kawo sauƙin kawar da tallafin ga 'yan kasuwa, waɗanda su ne: Shirin Bayar da Tallafin Kuɗi na Shugaban Ƙasa (PCGS), Asusun Tallafawa na FGN MSME, da Asusun Fannin Masana'antu na Gwamnatin Tarayya."
Ministan ya ƙara da cewa a wani yunƙuri na sauƙaƙa shiga shirin lamuni na ɗalibai, da magance ƙalubalen da ake fuskanta da kuma inganta yadda ake aiwatar da shi, Shugaba Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattijai takarda inda ya buƙaci a soke da kuma sake kafa dokar lamuni ta ɗalibai.
Daga nan sai ya yi alƙawarin cewa Shirin Zuba Jari na Jama'a zai dawo da ƙwarin gwiwa bayan an yi nazari sosai kan yadda ake tafiyar da shi, inda ‘yan Nijeriya da suka kammala karatun su a matakin gaba da Bautar Ƙasa (NYSC), da masu riƙe da OND za a riƙa biyan su alawus-alawus na wata-wata, ta hanyar Shirin Bayar da Lamuni na Jama'a har sai sun samu ayyukan yi.
Ya kuma ce shugabannin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da suka shuɗe ba su tafiyar da babban bankin yadda ya dace ba, amma Tinubu ya dawo da martabar babban bankin da ya ɓata.
"Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa ta fara samar da sakamako mai kyau, saboda tattalin arziƙin ƙasar yana farfaɗowa sannu a hankali, kuma matsalolin za su ƙare," inji shi.
Mun ciro kacokam labarin da hotunan daga shafin Mujallar FIM dake yanar GIZO da Facebook