Yan Ta’adda Sun Sake Sace Mutane 87 A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Kaduna
- Katsina City News
- 18 Mar, 2024
- 487
Masu garkuwa da mutane sun sake kai wani mummunan hari a kan wasu mutane a Kajuru- Station da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane 87 a daren ranar Lahadi.
Harisu Dari, daya daga cikin matasan tashar Kajuru, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kai harin da misalin karfe 10 na dare.
Rahotanni na cewa, maharan ba kawai sun yi awon gaba da mutane kadai ba ne, sun yi barna, inda suka shiga shaguna jama’a tare da kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hari da suka kai na sace mata 15 da wani namiji a yankin Dogon-Noma kwanaki kadan kafin wannan harin.
A kwanakin nan dai kananan hukumomin Kajuru da Chikun suna fuskantar sace-sacen jama’a daga mahara, wanda hakan ya jefa jihar cikin wani yanayi na tashin hankali.