Gwamnan jihar Zamfara ta Kaddamar da Asusun Kula da harkokin Tsaro
- Katsina City News
- 10 Mar, 2024
- 642
Gwamnatin Jihar Zamfara, ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal, ta ƙaddamar da ginin amintattun Asusun Kula da Harkokin Tsaro domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ta'addanci a jihar, inda Gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tallafa wa asusun ta kowane fanni.
A ranar Juma’ar nan ne Gwamna Lawal ya jagoranci ƙaddamar da ginin amintattun Asusun Kula da Harkokin Tsaro da ke Gusau babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce asusun tsaron na Zamfara yana ƙarƙashin jagorancin Tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda, MD Abubakar ne.
A cewar sanarwar, an ƙaddamar da aikin ne a ƙarƙashin wani kwamitin amintattu na ƙwararru a fannin tsaro domin aiwatar da aikin yadda ya kamata.
A yayin bikin ƙaddamar da ginin, Gwamna Lawal ya buƙaci sauran jihohin ƙasar nan da su kafa irin waɗannan asusun amintattu, da daidaita tsare-tsare, da samar da tsarin da ya shafi tsaron yankin.
Ya ce, “Yayin da Asusun Tallafa wa Tsaro ya fara aiki cikin tsari, ina roƙon a haɗa hannu da irin waɗannan asusu da wasu jihohi ke kafawa a yankunan su domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daƙile matsalar tsaro.
"Asusun yana da abubuwa da yawa da zai yi yayin da ya fara aiki. Wani abin da asusun zai ƙara mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da cire wa yaranmu da matasanmu tunanin rikice-rikice da kuma nuna ƙabilanci, wanda hakan ke haifar da tayar da ƙayar baya a wasu al'ummomi. Wannan ya zama dole don samun ci gaba mai ma'ana kuma mai ɗorewa.
“A ƙarƙashin jagoranci mai nagarta na Shugaban Asusun, IGP M.D Abubakar (Mai Ritaya) da sauran jiga-jigan kwamitin amintattun, muna sa ido ga haɗin kanku don haɓaka rayuwar jama’armu nan take.
“Mun dogara da ku, domin mun san ku duka kuna da cancantar ɗaukar irin wannan nauyi. Na gode da hidimar ku da aikin ku ga jihar ku.
“Abin da ke faɗo min rai a duk lokacin da aka kai wani hari, shi ne yabo bisa ƙoƙarin da Rundunar Kare Jama'a ta Zamfara, wacce muka ƙaddamar kwanan nan take yi wajen ceto al'umma.
"Muna da niyyar ci gaba da ƙoƙari wajen haɗa kan al'umma, ci gaba da wayar da kan jama'a, da kuma tabbatar da bin ƙa'idojin aiki da dukkan mambobin Rundunar Kare Jama'a ta Zamfara suka rantse a kai."