ZAMFARA TA KAMMALA AIKIN SHIRIN INGANTA LAFIYAR AL UMMAR JAHAR .

top-news


@ Katsina Times 

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na uku na Shirin Inganta Lafiyar al'umma Kyauta, inda aka duba mutane sama da 2,213.

Shirin na musamman da aka fara a watan Yulin bara, an samu nasarar duba lafiyar mutane masu fama da amosanin ido, gwaiwa, yoyon fitsari da aikin musamman tare da wayar da kan mutane sanin hanyoyin kauce wa kamuwa da cututtuka domin kiwon lafiyar su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa an duba lafiyar mutane sama da 2,213 a yayin shirin a matakin farko da na biyu da na uku.

A cewar sa, kashi na uku ya kasance tsakanin ranakun 23 zuwa 25 ga watan Fabrairun 2024.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ƙaddamar da wani shirin inganta lafiyar jama'a kyauta domin bayar da tallafin kiwon lafiya ga mabuƙata. Shirin yana ba da magani kyauta ga mutanen da ke fama da yanayin lalurar rashin lafiya ta yau da kullum kamar su amosanin ido, amosanin mara, gwaiwa da yoyon fitsari.

“Baya taimakon kiwon lafiya, shirin yana ilimantar da jama'a game da muhimmancin kiyaye lafiya da walwala. Wannan yunƙuri mataki ne mai kyau na inganta lafiya da jin daɗin al'umma gaba ɗaya.

“Ya zuwa yanzu an yi amfani da na'urorin zamani a shirin inganta lafiyar mutane 2,213 don ba da kulawa ta musamman ga majinyata daga karkara da birane, wanda ya ƙunshi ƙananan hukumomi 14 na jihar. Wannan tsarin ya bai wa marasa lafiya a wurare masu nisa damar samun kulawar kiwon lafiya da suke buƙata daga ƙwararrun likitoci.

“Shirin, a dukkan matakai, an samu masu lalurar gwaiwa 876, amosanin ido 931, da masu yoyon fitsari 84.

“Cibiyoyin da aka ware domin wayar da kan jama’a, sun haɗa da Babban Asibitin Gusau, Babban Asibitin Sarki Fahad, Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura, kuma za a tura dukkan waɗanda cutar tasu ta yi tsanani zuwa ga babban asibitin Tarayya da ke Gusau.”