Kwamitin Hana Boye Abinchi a Jihar Katsina Yayi Zama da Yan Kasuwa na Jihar Katsina
- Katsina City News
- 29 Feb, 2024
- 566
Shugaban kwamitin hana boye kayan abinci (Join Task Force) Alh. Jabiru Salisu Tsauri, wanda shine shugaban ma'aikatan gidan Gwamnatin Jihar Katsina yayi zaman ne yau 28 ga watan Fabrairu 2024, a dakin taron dake fadar gidan gwamnatin jihar Katsina, lokacin da yayi wani zama na musamman da shugabannin manoma, da kuma masu saye suna siyar da kayan abinci a fadin jihar Katsina.
A lokacin da yake jawabin makasudin zaman nasu yace domin wayar da kan su akan ayyukan kwamitin wanda suka hada da yin dokar dai-dai ta farashi, hana fitar da kayan abinci zuwa kasashen ƙetare, da hana boye kayan abinci domin samun kazamar riba. Sannan yayi karin bayani akan babu haramci ka siyo kaya daga wata karamar hukuma zuwa wata karamar hukumar dake cikin jihar Katsina.
A lokacin da yake amsa tambayar da wani dan kasuwa kuma Manomi yayi mashi game da makomar rumbunan ajiyar manoma da kuma masu siyo wa domin su siyar, Hon. Tsauri ya bayyana mashi cewa babu ruwan su da wajen ajiyar wanda ya noma ko kuma mai siye yana siyarwa, yace dokar zata yi aiki ne kawai akan wadanda suke siyo wa da farashi mai sauki su boye har sai yayi tsada sannan su siyar.
Shugabanin yan kasuwa da manoma da suka fito daga kungiyoyi na jiha da kuma kananan hukumomi talatin da hudu (34) na jihar Katsina ne suka halarci zaman.
Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
28/2/2024