Zamfara: Gwamna Dauda Lawal ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin sa don Inganta Ilimi

top-news


Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ganin ta kafa tubali mai inganci a harkar ilimi don ’yan baya su samu ilimi mai inganci a Zamfara.

Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata yayin gasar wasanni na shekara ta 2024 karo na uku na makarantar Almufida International Academy da ke Gusau.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa mai makarantar ya bai wa Gwamna Lawal lambar yabo a matsayin Babban Kwamandan Abokantaka na Kwalejin (GCFC).

Ya ce, Gwamnan ya yaba da yadda ɗaliban suka nuna ƙwazo a lokutan wasanni daban-daban.

A yayin jawabin nasa, Gwamna Lawal ya nuna jin daɗin sa ga yadda makarantar ke gudanar da ayyukanta na ɗora ɗalibai kan kyawawan halaye.

Ya kuma yaba wa ɗaliban bisa kyawawan wasannin motsa jiki, haɗin kai, da kuma ƙwarewar da suka nuna.

"Abin da na gani a nan ya burge ni, waɗannan halaye masu kyau suna nuna kyakkyawar makoma.

“Na zo ne a yau domin nuna goyon baya da nuna ƙwarin gwiwa wajen inganta fannin ilimi a jihar Zamfara. Idan dai za a iya tunawa, na kafa dokar ta-ɓaci a fannin ilimi da lafiya na jihar a wani shiri na gwamnati na.

“Shawarar mayar da martani ga ƙalubalen da harkar ilimi ta Zamfara ke fuskanta, mataki ne mai kyau na ganin ’yan baya sun samu ilimi mai inganci.

“Ilimi shi ne ƙashin bayan kowace al’umma, kuma Zamfara ba za ta iya yin watsi da shi ba.”

Gwamnan ya kuma zagaya, inda ya duba kayayyakin da kwalejin ta ke da su domin bunƙasa ƙwarewar ɗalibai.

NNPC Advert