Yanzu Muka Fara Kama ’Yan Tiktok, Cewar Hukumar Hisbah
- Katsina City News
- 13 Feb, 2024
- 673
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa yanzu ta fara kama ’yan matan Tiktok masu yada kalaman batsa.
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Mataimakiyar Babban Kwamanda Bangaren Mata, Dokta Khadija Sagir Sulaiman, a yayin da ake dakon gurfanar da fitacciyar ’yar TikTok din nan, Murja Ibrahim Kunya a gaban kotu.
Dokta Khadija ta bayyana cewa Hukumar Hisbah ba za ta nade hannu ta sanya idanu wasu ’yan mata suna cin karensu babu babbaka da sunan ’yancin soshiyal midiya ba.
“Ina yin amfani da wannan dama na ja hankalin sauran masu yin irin abin da Murja take yi a kafafen soshiyal midiya da su kuka da kansu su tuba su daina.
“Domin yanzu muka fara wannan kamen matukar ba su daina ba. Za mu fito da taimakon Allah sai mun kakkabe jiharmu mai albarka daga wannan badala”
Ta kuma nesanta Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ’yar TikTok din da mutane suke kallon ta a matsayin ’yar jamiyya wacce watakila ta fi karfin doka.
“Ni ina tabbatar wa duniya cewa kowa ya san gwamnanmu mai mutunci ne wanda ya fito daga gidan tarbiyya, ba zai taba goyon bayan barna ba.
“Hakan ne ma ya sa bisa umarninsa a watanni baya muka zauna da ’yan TikTok din inda muka yi musu nasiha a kan abin da suke yi.”
A cewar Mataimakiyar Babban Kwamandan, sun yi zama na musamman da Murja kan ta fadi abin da take so gwamnati ta yi mata wanda zai sa ta kame kanta amma ta ki ba su hadin kai.
“Mun nuna mata idan aure take son yi gwamna zai yi mata komai na aure, ko kuma idan tana son yin wani kasuwanci shi ma muka yi mata alkawari cewa gwamna zai ba ta jari, amma har muka tashi daga zaman ba ta gaya mana wani takaimemen abin da take so ba.
“A wannan zama bayan mun yi mata nasiha ta yi alkawari tare da sa hannu cewa ta daina abubuwan da take yi.
“Amma ga mamakinmu sai muka ga ta ci gaba da abin da take yi.”
Aminiya