An Kashe Mutum ɗaya an harbi ɗaya, an kuma sace Mata da ƙananan Yara a jihar Katsina
- Katsina City News
- 05 Feb, 2024
- 733
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Da Yammacin ranar Lahadi tsakanin Magariba zuwa Isha'i 'Yanbindiga suka kai hari a wani gari mai suna Katsalle a kusa da garin Mabai dake da nisan kilomita sha biyar (15) zuwa karamar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina inda suka Kashe wani mutum mai suna Mustafa, da jikkata wani mai suna Rabi'u tare da ƙona gidansa gaba ɗaya.
Haka kuma barayin masu garkuwa da mutane sun kwashi mata da ƙananan Yara da ya zuwa haɗa wannan rahoto bamu iya Tantancewa ba.
"Muna cikin tashin hankali bamu da wani sukuni muna ta addu'o,i a ko ina a masallatai, muna kuma neman dauki daga jami'an tsaro da Gwamnatin jihar Katsina, ɓarayin nan ƙara shigo mana kawai suke har a garin Mabai" inji Aqibu Abdullahi mazaunin garin da muka zanta da shi.
Duk da nasarorin da jami'an tsaron ke samu a wasu yankunan. Hare-haren 'yanbindigar a wasu yankunan na jihar Katsina yana kara ta'azzara ko a cikin satin da ya gabata ankai makamancin irin sa a Tashar Bawa dake kan iyakar Kaduna a karamar hukumar Sabuwa wanda yanbindigar suka kwashe fiye da mutum hamsin sukai garkuwa dasu.
Rahoton Katsina Times:
www.katsinatimes.com
07043777779, 08036342932