Amina Yarinyar da Dangin Iyayenta suka so Aurar da Ita ga Dan'tadda ta samu gatanci.
- Katsina City News
- 27 Jan, 2024
- 772
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Amina daga Karamar hukumar Danmusa da Bidiyon ta ya karaɗe kafafen sada zumunta akan Halin da ta tsinci kanta na Auren Dole ga mai garkuwa da Mutane ta samu gatanci wajen Gwamnan Katsina Malam Dikko Umar Radda.
Gwamnan na jihar Katsina ya karbeta a matsayin 'Yarsa ta hannun Uwargidan Gwamnan Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda, ya kuma bayyana riƙonta daga yanzu zuwa abinda hali yayi, kuma zata cigaba da karatu bisa kulawar mai bawa gwamnan Katsina shawara akan Ilimin 'Ya'yan Mata.
Itadai Amina Marainiya ce da take hannun Dangin Ubanta a garin Marke dake karamar hukumar Danmusa inda Iyayen suka amshi kayan Aurenta da nufin Aurar da ita ga barawo kamar yanda ta bayyana da bakinta.
Muna mika godiya da kuma fatan Alheri ga daukacin masu Aiko sako da kiran waya akan zasu dauki nauyin rayuwar ta zuwa Aure. Ta kafar mu ta Katsina Times, mungode a halin yanzu Amina tana hannun Gwamnatin jihar Katsina. Allah ya saka da Alheri.