MUSLIM MUSLIM TICKET: Mun dawo daga rakiyar gwamnatin Tinubu - Majalisar Shari'ar Musulunci
- Katsina City News
- 17 Jan, 2024
- 611
Majalisar ƙoli kan harkokin shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda ta ce an yi watsi da muradun Musulman ƙasar.
Majalisar ta bayyana haka ne a wajen taron da ta kira na kwanaki biyu a Abuja domin nazari kan abubuwan da suka biyo bayan zaɓen 2023 a Najeriya.
Babban magatakardar majalasar, Nafiu Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa majalisar ta kira taron ne saboda sauraron ƙorafe-ƙorafe na ɓangarori daban-daban da mutane ke da shi sakamakon abubuan da suka biyo bayan zaɓen 2023 a Najeriya.
'Mu ne muka yi jagorancin tattara ƙungiyoyin Musulmi da malamai don su goya wa tikitin da ya kai wannan gwamnatin ga samun nasara, kuma malamai da ƙungiyoyin addini yanzu suna fitowa suna cewa an kai su an baro, an yi 'Muslim-Muslim tiket' amma an yi watsi da muradin Musulmi da waɗanda suka sha wahalar zaɓen gwamnatin'. In ji shi.
Ya yi bayanin cewa taron dama ce da dukkan ƙungiyoyi da jama'a za su iya zuwa domin su bayyana duk wata matsala da suke da ita da wannan gwamnatin, ganin cewa mafi yawansu ba a cika masu alƙawuran da aka yi ma su ba, har a da ita kanta majalisar.
'Babu wanda ya fi mu ƙorafi, domin mun tashi mun bayar da duk gudunmawarmu ga samun nasara, amma ko 'sannunku, mun gode' babu wanda ya ce mana, haka ake siyasa? Sa'annan kuma duk abubuwan da muke ganin muradi ne na Muslmi da Musulunci an yi watsi da su, sai waɗanda suka yi adawa da wannan 'Muslim-Muslim tiket' su ne ake bai wa ribar nasara da aka samu.'
Magatakardar ya ce majalisar ta ɗan yi nadamar goyon bayan da ta bada soboda a cewarsa; 'Mun tura mota ta tashi ta buɗe mu da ƙura da hayaki, ta tafi ta bar mu a tsaye,'
Ya ce dole ne idan dama irin wannan ta sake samuwa a sake zurfafa tunani kafin yanke shawara.
Game da maganganun da ya ce wasu mutane na yi na cewa majalisar ta sayar da mutuncinta, Baba Ahmed ya musanta wannan inda ya ce a koda yaushe suna ƙokarin jawo hankalin gwamnati idan har ta yi ba daidai ba.
Ya ce' Shi kanshi shugaban ƙasan mun kalli fuskarsa mun faɗa masa cewa bai kyauta ba, don bai cika alƙawari ba amma duk mutane ba su san wannan ba.'
Ya ce tattaunawar za ta bada damar samun fahimta tsakanin majalisar da al'umar Musulmin ƙasar domin a sami daidaito wurin shawarwarin da za a yanke nan gaba.
Daga Shafin BBC Hausa