‘Yan Ta’adda Sun Sace Uba Da ‘Ya’yansa Mata Uku A Jihar Zamfara, Sun Bukaci Naira Miliyan 100 Kuɗin Fansa.
- Katsina City News
- 15 Jan, 2024
- 715
Wasu gungun ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Sabiu Abdulkadir tare da ‘ya’yansa mata uku a gidansu da ke unguwar Damba a Gusau babban birnin jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wani mazaunin unguwar mai suna Aliyu, sace Alhaji Sabiu da ‘ya’yansa mata, Hadiza, Fateema da Aisha a lokacin da ‘yan ta’addan suka mamaye yankin Damba a ranar Talatar da ta gabata.
Mazaunin garin ya ce ‘yan ta’addan sun tuntubi iyalan Alhaji Sabiu a ranar Asabar inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 100 domin kubutar da mutanen.