Tinubu na fuskantar matsin lamba don dakatar da Betta Edu
- Katsina City News
- 07 Jan, 2024
- 634
Kwanaki ƙalilan bayan hukumar EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar jin-ƙai ta Najeriya Sadiya Umar Farouk kan zargin ɓarnatar da wasu kuɗaɗe, sai ga shi sabuwar ministan jin-ƙan, Betta Edu na ƙoƙarin wanke kanta daga zargin sabuwar badaƙala a ma'aikatar.
Hakan na zuwa ne bayan fitar wata takardar biyan kuɗi da ministar ta aike wa ofishin babbar akanta janar da ƙasar, inda a ciki take buƙatar a tura zunzurutun kuɗi har naira miliyan 585, 189,500, don biyan tallafi, a wani ɓangare na tallafa wa masu tsananin buƙatar tallafi a wasu jihohin kasar huɗ.
To sai dai wani abu da ya ja hankali game da biyan kuɗaden shi ne sunan asusun bankin da aka biya kuɗin na wata mata ce mai suna Onlyelu Bridget Mojso.
Tuni dai ofishin babar akanta janar ta ƙasar ya ce ba ya biyan kuɗin gudanar da wani aiki na gwamnati a asusun wani mutum.
Wannan batu dai ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar musamman a shafukan sada zumunta inda mutane da dama ke kiran shugaban kasar Bola Tinubu ya sauke ministar daga mukaminta
Wani mai amfani da shafin X mai suna Waspapping_ya ce ''inda har aka kai safiyar gobe Beta edu na kan matsayinta, to za mu son cewa Bola Ahmed Tinubu bai shirya wa jagorantar ƙasar nan ba. Babu yadda za a yi ka dakatar da Halima Shehu sannan ka bar Betta Edu, wadda ake da manyan zarge-zarge a kanta ba, ka dakatar da ita yanzu, sannan ka bar EFCC su gayyaceta domin tuhumarta.
Shi ma wani mai amfani da shafin X mai suna TahaAdamy cewa ya yi ''Kamar Halima, ya kamata a dakatar da Betta Edu, a binciketa, sannan a gurfanar da ita idan an same ta da laifi. Ya kamata shugaban ƙasa ya rushe ma'aikatar jin-ƙai, saboda tana neman zama wata matattarar cin hanci ga mutanen da suka jagorance ta a baya da kuma yanzu, a ƙarfafa hukumar NEMA don aiwatar da ayyukan hukumar.
A nata ɓangare ministar jin-ƙai Betta Edu ya musanta zargin, tana mai bayyana shi a matsayin maras tushe balle makama.
Ministar ta kuma ce wannan batun tuggun masu kawo ruɗani ne da ke ƙoƙarin ganin sun dankwafar da ƙoƙarin da ma'aikatarta ke yi wajen kawar da cin hanci da rashawa.
A farkon wannan makon ne hukumar EFCC ta gayyaci dakatacciyar shugabar hukumar bayar da tallafin dogaro da kai ta Najeriya, NSIPA, Hajiya Halima Shehu kan zargin badaƙalar kuɗaɗe.
Rahotonni na cewa Hajiya Halima ta tra wasu kudi kimanin naira biliyan 40 daga asusun hukumar NSIPA zuwa wasu asusu mallakin wata mata da kuma wani kamfani na daban.