ZARGIN KWATAR FILAYE: FITINA NA TAFASA A GARIN BARHIM. ...An roki gwamnan Katsina ya saka baki.
- Katsina City News
- 14 Dec, 2023
- 646
Muazu Hassan @ Katsina Times.
Al ummar yankin garin Barhim da suke zargin wani kamfani ya kwace masu filaye da gonaki domin gina gidajen masu hannu da shuni, sun bayyana cewa yanzu zasu dau mataki na gaba tun da bin tsarin doka da zaman lafiya yana neman cin tura.
Al ummar sun yanke wannan shawarar ne, bayan wani taro da suka yi a jiya laraba 13/12/2023.kuma suka turo wakilai su zo har kamfanin jaridun Katsina Times don bayyana ma duniya matsayar da suka dauka.
Wakilan da suka zo, sun ce da aka fara matsalar sun dauki lauya Wanda ya kai kotu kuma ya mika takarda ga duk inda ya dace.amma mai makon a rika girmama su a matsayin masu bin doka, sai aka gayyato yan daba daga wata karamar suke musguna masu.
Al ummar sun ce, zama mutamin Kirki sai Wanda ya zaba, amma kowa na iya zama dan tasha.
Al ummar sun ce, hatta kotu ta tsayar da aikin amma wani da yake jin yafi karfin doka ya rika dibar kasa a wajen ya kuma sanya "yan banga suna tayi masu barazana.
Katsina Times ta gano Wanda yake aikin wani dan kasuwane, Dan asalin karamar hukumar kurfi mazaunin Abuja.kuma dai dai lokacin da ake wannan takun saka, mai iya zama fitina, shi yana filin jirgin saman Katsina, zai koma Abuja inda yake zaune da iyalinshi.
Lauyan dake tsaya mutanen yace gwamnan Katsina Malam Dikko Umar Radda ne kawai zai iya warware wannan takaddama da ke neman zama fitina.
In zamu iya tunawa, mutanen wannan yankin da suke zargin an kwace masu filaye sunyi wani taron manema labarai ranar talata 12/12/2023.cikakken bidiyon taron yana nan a shafin Facebook da YouTube na Katsina times da Katsina city news.
Katsina Times
@www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779.08057777762