KO NADIN ‘RECTOR’ NA HASSAN USMAN POLYTECHNIC YA SABA WA DOKA?
- Katsina City News
- 13 Dec, 2023
- 771
…Na cika duk wasu ka’idoji -Rector
Mu’azu Hassan @Katsina Times
Jaridun Katsina Times sun samu wani korafi na neman tababar cancantar Aminu Kalla Doro a matsayin Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman da ke Katsina, korafin da wata kungiya ta rubuta da sa hannun mutane biyar.
Masu korafin sun yi zargin cewa Aminu Kalla bai kai matsayin karatun Dakta ba, kuma lokacin gabatar da sunayen wadanda suka yi jarabawar zama Rector, sunansa kadai aka gabatar dag sashen Kula da Ilimi Mai Zurfi (Deparment of Higher Education) ta Jihar Katsina.
Jaridun Katsina Times sun bi diddigin lamarin kamar yadda masu korafin suka kawo koke kuma suka nemi a bincika.
A ranar 9 ga watan Mayu, 2023 aka sanar da bai wa Aminu Kalla Doro a matsayin Rector na Hassan Usman Katsina Polytechnic. Sanarwar ta biyo bayan amincewar Gwamnan Katsina, na lokacin Alhaji Aminu Bello Masari CFR, kamar yadda Dokar makarantar ta tanada.
Takardun nadin da jaridun Katsina Times suka gani, sun nuna da cewa shugabar Kwamitin Gudanarwar Kwalejin, Hajiya Indo Muhammad (MFR) ta rubuta wa Gwamnan Katsina takarda a ranar 3 ga Mayu, 2023.
A cikin takardar take cewa, mutane tara suka rubuta bukatar neman zama shugaban Kwalejen, amma sun sallami mutane biyar don ba su cancanta ba.
A ranar 4 ga Afrilu sun gana da mutane hudu. Mutane uku sun yi nasara a jarabawar da aka yi masu, kuma dukkaninsu sun cancanta.
Rahoton tsaro a kan su ukun ya wanke su a kan suna iya zama shugabannin Kwalejin in an zabe su.
Takardar ta ci gaba da cewa, Aminu Kalla Doro shi ne ya zo na daya, Dakta Aminu Bello A. Birchi ya zo na biyu, sai Muhammad Jalalu Maiwada ya zo na uku.
Takardar sai ta kara da cewa Hukumar Gudanarwar Kwalejin na ba da shawarar a zabi Aminu Kalla Doro da ya zo na daya, kuma shi ne ke rike da mukaddashin shugaban makarantar a lokacin.
A takardun da jaridun Katsina Times ta gani, a ranar 4 ga Mayu, 2023 mai ba Gwamnan Katsina shawara a kan Ilimi mai zurfi, ya rubuta wa Gwamnan takarda bisa dogaro da matsayar da Hukumar Kwalejin ta dauka na amincewa a bai wa Aminu Kalla Doro shugabancin makarantar, a matsayinsa na wanda ya zo na daya a jarabawar da aka yi ta zaben Rector.
Bisa dogaro da wadannan takardu guda biyu, Gwamnan Alhaji Aminu Bello Masari CFR ya amince da nadin Aminu Kalla Doro a matsayin Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina a ranar 9 ga Mayu, 2023, kamar yadda sanarwar da aka fitar ta nuna.
INA MATSALAR TAKE?
Wasu takardu na ka’idojin nadin Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, wadanda jaridun Katsina Times suka samu, sun ga cewa an karfafa maganar mai matsayin karatun Dakta ga duk Wanda za a baiwa mukamin shugaban makarantar kimmiyya da fasaha.
Takardar ka’idar farko ita ce ta Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya (Federal Ministry of Education), a kan ka’idar zaben Shugaban Kwalejin, Magatakarda, Jami’in Kula da Kudi (Kashiya), Mai Kula da Dakin Karatu, da Mataimakin Shugaban Kwalejin na duk Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ake da su.
A wannan ka’idar an ce, dole wanda za a nada Rector na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) ya zama yana da matsayin karatu na Dakta (PhD). Wannan ka’ida an kara jaddada ta a shekarar 2022.
Wata takardar da jaridun Katsina Times suka gani ita ce, Hukumar da ke kula da Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na Kasa (National Board for Technical Education) takardar mai taken: “Ka’idojin zaben Rector, Registrar, Librarian da kuma Bursar a duk Polytechnic da ke Nijeriya.” Ka’idar an amince da kara jaddada ta a ranar 27 ga Maris, 2023. A cikinta aka ce, ba wanda za a ba Rector a Kwalejin Kimiyya da Fasaha sai mai matsayin karatun Dakta in ba Dokta to a baiwa cif lakchara.
A ranar 30 ga Oktoba, 2023, Hukumar NBTE ta rubuta wa duk Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na Tarayya da na Jihohi da kuma masu zaman kansu cewa, su tabbatar sun bi ka’idojin da Hukumar ta amince da su na zaben Rector da sauran masu ruwa da tsaki na Kwalejojin.
Takardun ka’idojin da jaridun Katsina Times suka gani, sun nuna an ajiye ka’idar matsayin matakin karatun Dakta a zaben Shugaban Kwalejin Hassan Usman Katsina.
BA NI NA ZABI KAINA BA, NA CIKA DUK KA’IDOJI
Jaridun Katsina Times sun tuntubi Malam Aminu Kalla Doro domin jin ta bakinsa, inda ya shaida mana cewa ya cika duk ka’idojin da Doka tanada.
Ya ce lallai shi ba Dokta ba ne, amma Babban Malami (Chief Lecture) ne da yake kan wannan matsayin tun a shekarar 2012. Ya ce ka’idar NBTE cewa ta yi mai mukamin Dakta, ko kuma wanda yake da matsayin Chief Lecture.
Malam Aminu Kalla ya kara da cewa; “Jarabawa aka yi ni na zo na daya, Hukumar Gudanarwar Kwalejin nan ta tura sunayenmu mu uku, aka dauki nawa da yake ni na zo na daya.”
Aminu Kalla ya kara da cewa: “Ba ni na nada kaina ba, doka da ka’idar da aka tsara ta kai ni matsayin na Rector.”
Katsina Times
@www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762