Fiye Da Mutum 2700 Ne A Ka Kwace Wa Gonaki Da Filaye A Kauyen Barhim . Sunyi Kira Ga Dikko Radda Ya Shiga Lamarin A Maido Masu Hakkin Su
- Katsina City News
- 12 Dec, 2023
- 616
Zahraddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Al'ummar Kauyen Barhim dake cikin Karamar hukumar Batagarawa a Jihar Katsina sun koka akan yanda aka kwace masu gonakin da filaye da suka ce yakai Hecta 78 kuma Fiye da Mutum dubu biyu da Dari Bakwai ne mamallakan Wajen sun gaje Shi Tun Iyayensu nan suke Nomawa kuma suna sauran Mu'a malolinsu a wajen fiye da shekaru Tamanin. Suka ce suna da shedar Mallakar Wurarensu a Gwamnatance, amma da rana tsaka cikin damunar Bara, sunyi Noma ya Fidda Kai amfani ya kawo, kawai sai suka ga anzo da mota An share wajen, wai aka ce Gwamnati ta Kwace Wajen, ba a sanar da su ba, ba zato babu tsammani.
Mutanen Kauyen na Barhim Sun koka matuka, kuma sun mika koken nasu ga duk wasu Hukumomin da zasu taimaka masu don hakkin su ya dawo garesu, suka ce amma har yanzu shiru.
Suka ce a dalilin haka yasa suke rokon Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda da ya duba matsalolin su, inda a dalilin kwace masu Filaye da gonaki, wasu sun fada mawuyacin hali wasu ma hawan jini ya kamasu suna jinya a Asibiti.
Suka ce a halin yanzu haka an kawo ma'aikata da Bulaluwa an fara aiki a cikin filayen nasu, suka ce a da an kawo 'yan sanda suna gadin Wajen amma da suka turo koken su ga hukumar 'yan sanda su kansu suka gane babu kyautaw a ciki sai suka janye ma'aikatan su. Suka ce "Yanzu sun kawo 'Yan Katsina Community Watch da aka dauka don kare Al'umma yanzu sunzo suna gadin gonaki, suna kuma bugun Mutane da Kullesu hadda Kwace masu Kudi, idan suka nuna an kwace masu Filaye."
Da Katsina Times take zantawa da daya daga cikin Lauyoyin Masu gonakin Barista Muhammad Muhammad, ya bayyana takaici akan yanda aka akwa kwace Fili mai girma kamar wannan aka mallaka ma Mutum daya, yace "Eh Doka ta bawa Gwamnatin dama ta iya amsar fili ta aiwata da abinda take so dashi, amma sai idan abin zai Amfani al'umma ne, ko kuma an gano wani arzikin karkashin kasa a wajen da makamantansu.
Barista Muhammad Muhammad ya Zargi Wani Sobeya Janaral, Abdu Manaja da wani ma'aikacin sa Saifullahi yace su ne suka jagoranci cire duk wata alama da ke cikin ginakin. Yace sun shigar da kara akansu a Kotun Batagarawa wanda kotu ta zargesu da laifin saba ka'ida da barnata Dukiya, kuma kotu ta nemi su gurfana a gabanta sun gudu, yace "Amma abin mamaki duk da haka gashi ana ci-gaba da kawo kayan aiki ana ta aiki a wajen.
Barasta Muhammad Muhammad yace kai tsaye suna so aimasu karin bayani cewa minene matsayin Takardar shedar Mallakar Filayen da Wadannan bayin Allah suka mallaka daga Gwamnatin tunda ga wasu sunzo sunce wai su ne keda filayen kuma gwamnatin ce itama ta basu.