Ƙungiyar ‘Yan Jaridu Ta Taya Sabon Shugaban Gidan Rediyon Katsina Murna
- Katsina City News
- 12 Dec, 2023
- 658
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta ƙasa NUJ reshen jihar Katsina ta taya murna ga ɗaya daga cikin ɗan ƙungiyar Alh. Lawal Attahir Bakori bisa naɗashi da akayi a matsayin shugaban gidan Rediyon jihar Katsina.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na jihar Tukur Hassan Dan-Ali ya sanya wa hannun a yau 12/12/2021.
Ƙungiyar ta godewa Gwamna Dikko Umar Radda na naɗa ɗaya daga cikin ɗan ƙungiyar Lawal Attahiru ya zama shugaban gidan Rediyon.
Kungiyar za ta ci gaba da yin aiki tare da sabon shugaban da nufin tallata manufofin Gwamnatin jihar.
Ƙungiyar ta bayyana naɗin Lawal Attahiru a matsayin ɗaya daga cikin wadanda suka cancanta.
Daga karshe kungiyar tayi addu’ar Allah ya yi wa sabon Manajan gidan rediyon jagora.