AGILE BATA DA MATSALA. Inji shiek Mahmood Gumi

top-news


 "The Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment, (AGILE) Project wani shiri ne da Bankin Duniya ke tallafawa Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya wanda aka tsara don inganta guraben karatun sakandare ga 'yan mata masu tasowa tsakanin 10 zuwa 20."

" Duk wanda ya ke da'awar akasin haka, to ya nuna inda shirin ya sabawa Musulunci ba wai kawai adunga cusa kyama da kiyayya ga abu ba. Yin Allah wadai da wani aiki da za a yaba ba zai kawo komai ba sai tabarbarewar yanayin lafiya, zamantakewa da al'adun 'ya'ya mata a cikin al'ummarmu."

 "Wasu mutanen karya ce kawai da son zuciya suke a cikin faɗakarwa.  Don haka ne suka hana talakawa allurar riga-kafin cutar shan inna, a yau bayan kokarin da gwamnati ta yi, Nijeriya ba ta da cutar shan inna – alhamdulillahi."

 Shin sun fi son wadannan ’yan mata su zama masu sana’ar abinci ko  Talla a Titi  da kasuwanni ko kuma su na so su kasance a ajujuwa suna koyon zama likitoci, ma’aikatan jinya da malamai?

" Lallai Musulunci addini ne na ilimi ga dukkan jinsi, kuma haramun ne a bayyana wani sabon haramiya ba tare da bin diddigin addini ba."

" yarinya za ta iya samun ilimin zamani ba tare da tabar dabi'un addini da al'adu ba, wannan abin da AGILE take kenan."

 Allah ka tsare mana yaran mu mata daga jahilci da sakaci.  Amin.