Sarkin Katsina Bai Kori Shirin AGILE / WB Project Katsina. Ba...
- Katsina City News
- 09 Dec, 2023
- 1276
Mai Martaba Bai Kori Shirin AGILE / WB Project Katsina. Ba...
Bisa ga Bayanai da na samu daga fadar mai martaba sarkin Katsina sun tabbatar da cewa mai martaba bai ce ya kori shirin Agile a jihar Katsina ba, illah dai yace masu jagorancin shirin a jihar Katsina sunje Masarautar amma dai ya kafa ƙwamitin tuntuba akan shirin.
Sarkin Labarai na Masarautar Malam Ibrahim Bindawa yace masarauta ta kira taron tuntuba wanda ya haɗa da dukkanin Malamai na kowane ɓangare da kuma jami'an shirin a jihar Katsina.
Bindawa ya ƙara da cewa shi da kanshi ya rarraba takardun gayyatar wannan taron tattaunawar, amma dai babu inda masarauta tace ta kori shirin Agile baki ɗaya daga jihar Katsina.
Shi kanshi Shugaban shirin a jihar Katsina yace basu da wata masaniya ta korar shirin a jihar Katsina daga Masarauta ko kuma daga Gwamnatin jihar Katsina, hasalima ita Gwamnatin jiha itace keda alhakin shirin ba Masarauta ba.
Wani mai sharhi akan harkokin yau da kullum yace wannan shirin shiri ne na Gwamnatin Tarayya haɗin guiwa da Bankin Duniya tare da Gwamnatin jiha dan haka Masarauta ba ta da hurumin korar shirin, Mai yiyuwa dai ba a fahimci saƙon Masarautar ba a cewar shi.