Kungiyar Malamai ta Ƙasa NUT Ta Yi Sabon Shugabanci a Jihar Katsina
- Katsina City News
- 06 Dec, 2023
- 944
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Aranar Laraba 6 ga watan Disamba 2023 Kungiyar ta "Nigerian Union Of Teachers" (NUT) Shiyyar Katsina ta gudanar da wani gagarumin taron ta na jiha da Walimar zuwan sabuwar shugabar tasu Hajiya Rakiya Shehu Runka.
Kafin Zamanta shugabar Kungiyar, Hajiya Rakiya Shehu Runka Uwargidan Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dokta Mustapha Inuwa kuma shugabar Makarantar Sakandare dake Ajiwa, ta kasance mataimakiyar Shugaban Kungiyar ta NUT, inda daga bisani 'Ya'yan kungiyar ta jihar Katsina suka nuna sha'awar su ta zama shugabarsu kamar yanda Dokokin kungiyar suka tanada.
A Zantawar ta da Jaridar Katsina Times Hajiya Rakiya ta yi godiya ga Allah da ya azata bisa wannan dama da ta samu, tace "duk da itace mace ta farko da ta rike wannan kujera abin ba zai zamar mata bako ba, duba da ta taba zama shugabar Faransifal (Principal) ta jihar Katsina.
Sana Hajiya Rakiya ta mika godiyarta ga Gwamnatin jihar Katsina bisa Jagorancin Gwamnan jihar Dokta Dikko Umar Radda, inda ta bayyanashi a matsayin mai matukar kishin ilimi da son cigaban malaman makaranta.
Sana Rakiya tayi godiya ga Membobin Kungiyar NUT bisa dama da kuma hadin kai da suka bata, gami da kauna da suka nuna mata har ta kasance a matsayin shugabar su.
Hajiya Rakiya ta sha alwashin kawo sauye-sauye a cikin kungiyar da kuma tabbatar da ganin malamai sun cigaba da samun horo don koyarwa mai inganci.
Hajiya Runka ta bayyana yanda zata fara salon Jagorancin ta da bin makarantu don karama malamai karfi da kwarin gwiwa akan yanda zasu dunga koyarwa kamar yanda Gwamnati ta tsare masu hakkokin su.
Sana kuma zata tabbatar da jindadin malamai a duk inda suke a fadin jihar Katsina musamman zuwa karo Ilimi da sauransu.
A karshe ta yi kira ga mata musamman akan jajircewa don ganin sun cimma nasara ta rayuwa, kuma Hajiya Rakiya Shehu Runka ta yaba wa mijinta Dokta Mustapha Inuwa akan dukkanin nasarorin da ta samu, tace da bai yadda ba da ba zata samu wannan nasara ba, inda tayi kira ga sauran mazaje da suyi koyi da irin kwarin gwiwa da mai gidan nata yake bata.
Da muke zantawa da wasu daga cikin Mambobin kungiyar ta NUT sun bayyana jin dadi da fata bisa wannan sabon Jagorancin da suka samu. An gudanar da taron ne ofishin kungiyar ta NUT dake kusa da Ofishin Kula da gidajen Mai na jihar Katsina (NMDPRA)