Kada Tinubu da Ganduje su yi wasa da wuta a Kano
- Katsina City News
- 30 Nov, 2023
- 612
Gargadi daga Farfesan Turanci Farooq A. Kperogi daga Amurka
Daga Farooq A. Kperogi (Twitter: @farooqkperogi)
Fassarar Danlami Musa (07018374765)
A cikin tsarin shari’ar da aka yi hasashe, aka tsattsara, kuma aka bi shi daki-daki, kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta yanke, wanda ya sauya nasarar zaben gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Yusuf. Ina fata da gaske cewa wannan cin zarafi na adalci ba shi ne tartsatsin da zai kunna wuta a Kano ba—da kuma kasa baki daya.
Alamu sun bayyana tun farkon watan Oktoba cewa an yanke shawarar cewa ba tare da la’akari da gaskiyar lamarin ba, dole ne a kiyaye kurakuran da aka riga aka shirya a yanke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ta kowane hali.
Misali, a ranar 6 ga Oktoba, Shugaban Sashen Shari’a na INEC a Jihar Kano, mai suna Suleiman Alkali, ya rubuta wata wasika mai ban mamaki, inda ya bayyana cewa INEC, wadda ta bayyana Yusuf na NNP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Kano, ba ta da sha'awar kare ayyanawar ta.
"Hedikwatar hukumar ta umurce ni da cewa INEC a matsayinta na Hukuma ba ta da wani dalilin daukaka kara a kowane hukunci," ya rubuta. “Saboda haka, hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa da kuma Kwamishina na kasa mai kula da shiyyar Kano ta ba da umarnin a janye daukaka karar sannan a mika duk wani tsari na duk wani kararraki ga ofishin Kano.”
Da yake mayar da martani kan bacin ran da wasikar ta haifar, Sam Olumekun, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ya ce, Alkali ba shi da ikon rubuta wasikar, yana mai nuni da cewa “tuni aka janye wasikar kuma an ladabtar da jami’in.” Ba a gaya mana yanayin "tsawatarwar" ba saboda ƙarya ce.
Irin wannan dai shi ne abin da ya faru lokacin da INEC ta hada baki da Ahmed Lawan don kwace nasarar zaben fid da gwani na kujerar Sanata na yankin Yobe ta Arewa da dan takarar APC Bashir Machina ya lashe, wanda Kotun koli ta tabbatar, a wani abin rashin kunyar da na kira fashin daji na shari’a.
(Mai Shari’a Musa Dattijo Muhammed mai ritaya ya nakalto kalaman da abokin aikin nasa ya yi na cin mutuncin Kotun koli a lokacin da yake bankwana da abokan aikinsa, duk da cewa shi da takwaransa ba su nuna nakalto ni suka yi ba—kuma ya dan yi kuskuren nakaltowar. Na fada a makalar ranar 6 ga Fabrairu mai taken "Lawan da Kotun Koli na 'Yan fashin dajin Shari'a marasa kunya" cewa, "Babu shakka Kotun koli ta Najeriya rubabben taron 'yan fashin dajin shari’a ne da ake iya saye. Wanda ya fi ba da kudi mafi tsoka ne yake samun hukuncinsu.")
Ko ma dai menene, a ranar 5 ga Satumba, 2022, wani lauyan INEC mai suna Onyechi Ikpeazu, SAN, ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya domin bata sakamakon zaben da ya bayyana Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwanin Sanatan Yobe ta Arewa.
Bayan kaduwa da fusatan da suka biyo bayan wannan, Festus Okoye, a lokacin kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ya musanta takardar da Ikpeazu ya yi, ya kuma ce, “Hukumar za ta sake duba ka’idojin tabbatar da ingancinta, ciki har da ta hanyar manyan jami'an da suka dace na duk matakan da aka shigar a madadinta don tabbatar da daidaiton su a cikin dukkan bayanan tare da dukkan rahotannin da ke hannunsu kafin gabatar da su don kada a sake maimaita irin wannan yanayi."
To, a cikin watan Oktoba na wannan shekarar an sake yin irin wannan lamarin a Kano, kusan shekara guda ke nan. Yana da alamar tsarin aiki da kyau. INEC ta fara ne da daga filfilo, in ta ga yadda yake tashi, sai ta fado da shi kasa. Amma duk abin da ake nufi shi ne shirya tunanin jama'a game da abin da ake ƙirƙira ta yadda za a rage girman kaduwar da zai haifar idan ya kasance a ƙarshe.
Idan har sakamakon shari’ar Ahmed Lawan da Bashir Machina ya kasance jagora, hakan na nufin INEC na da hannu dumu-dumu a cikin harkallar Ganduje tare da kulla makarkashiyar kwace nasarar Gwamna Yusuf. Haka nan yana iya nufin cewa "'yan fashin dajin shari'a" da na yi magana game da su a Kotun koli suna jira a cikin fuka-fuki don yin wani cin abincin dare na zaben da aka sace. Ina fatan na yi kuskure.
Alama ta biyu da ke nuna cewa wannan hukunci na kotun daukaka kara ya kasance wasan kwaikwayo ne da aka yi nazari a kai ya zo ne bayan da kotun ta gama tattaunawa kan hukuncinta a ranar 6 ga watan Nuwamba, amma ta dage zaman yanke hukuncin har zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, sannan ta bukaci a kara tsaurara matakan tsaro a Kano da zummar bayyana hukuncin da ta yanke. Mutanen da ke cikin gudun yi wa adalci karan tsaye ne kawai ke neman kariya ta kandagarki daga waɗanda ta’asarsu ta shafa.
Kamar yadda na yi nuni a filin rubutu na na ranar 23 ga Satumba, 2023 mai take “Abin da ya sa hukuncin Kano ba zai iya tsayawa ba,” a bayyane yake cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa a yanzu, Abdullahi Ganduje ya kuduri aniyar yin watsi da duk wani abin da zai biyo baya, tare da amfani da karfin gwamnatin tarayya don kwace ikon da jam’iyyarsa da dan korensa suka rasa a hannun Rabi’u Kwankwaso da surukinsa a zaben gwamna.
"APC ta bayyana aniyar dawo da abin da ta rasa ta akwatin zabe ta hanyar magudin shari'a," na rubuta. "Wannan wani tsari ne mai girma, mafi nagarta, kuma wanda ba gidadanci irin wanda suka yi a zaben 2019, bayan tsohon Gwamna Abdullahi 'Gandollar' Ganduje ya sha kaye a hannun shi dai Abba Yusuf din."
A cikin rashin mutunta sakamakon da hakan zai iya haifarwa na rashin tabbas, Ganduje—hakika, tare da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu—ya yanke shawarar yin duk mai yiwuwa don kwace nasara ta hannun shari’a daga shan kayen zaben.
Kamar yadda zan nuna nan ba da jimawa ba, kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara ba su ma nuna kamanta adalci a hukuncin da suka yanke ba. Tuni aka ba su hukuncin da ake so, kuma aka ba su umarnin su yi fatsan hujjar tabbatar da hakan. Hukuncin shi ne, tabbas, dole ne Abba Yusuf na NNPP ya tafi, kuma Nasiru Gawuna na APC ya maye gurbinsa.
A cikin karatun barkwanci, muna kiran wannan wasan ƙarshe, wato, ƙarshen da ke neman shaida. Masanan ilimin halayyar dan Adam suna kiran sa "tunanin da aka kwadaitar," wato, fassara mai raɗaɗi da gangan da aka tsara don haifar da ƙaddararren sakamako. Masana Falsafa suna kiran waccan ‘yan ba-ni-na-iya, wato tunanin da ya yi watsi da shaida.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito mai shari’a Moore A. Adumein ne ya yi hasashen rushe nasarar da Yusuf ya samu kan rashin kasancewarsa dan jam’iyyar NNPP a lokacin da jam’iyyar ta tsayar da shi takara. "Kamar yadda aka samu, Yusuf Abba ba dan jam'iyyar NNPP ba ne a lokacin da ake zargin jam'iyyarsa ce ta dauki nauyinsa, kuma bai cancanci tsayawa takarar gwamnan jihar a watan Maris ba," in ji Justice Adumein.
Amma duk da haka a soke zaben dan majalisar wakilai ta APC Musa Iliyasu Kwankwaso tare da mayar da Yusuf Umar Datti na NNPP a matsayin sahihin zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kura/Madobi/Garun Malam na Kano, kotun daukaka kara ta ce makonni biyu da suka gabata “batun zama mamban jam’iyyar siyasa al’amari ne na cikin gidan jam’iyya, wanda babu wata kotu da ke da hurumin shari’a a kansa,” a cewar jaridar LEADERSHIP.
Na yi tunanin cewa wannan zaunanniyar doka ce. Kamar yadda na rubuta a wani filin rubutu na da ya gabata, “Hukuncin da Kotun koli ta yanke ranar 26 ga Mayu, ya kuma ce jam’iyyun hamayya ba su da hurumin yin tambaya kan ingancin hukuncin cikin gida da wasu jam’iyyu suka yanke, sai dai idan sun tabbatar da cewa sun gamu da barna a sakamakon hukuncin cikin gidan da wata jam’iyyar ta dauka.” Don haka hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke kan wannan batu matacce ne kamar gawa idan an daukaka kara.”
Abin tambaya a yanzu shi ne, me ya sa Yusuf na NNPP ake rike da shi da wani matsayi na daban? Na samu cewa Kwankwaso da Yusuf ba su ririta nasarar da suka samu da kyau ba. Maimakon su yi farin ciki, nasarar da suka yi ta tado da mugunyar fansa da mugun nufin da ke cikin su. Amma wannan ba dalili ba ne na satar nasarar da suka samu ta halal
Ina da yakinin cewa NNPP za ta kai wannan karar zuwa Kotun koli. Idan har Kotun koli ta kasance tana bin ka'idojinta, wanda ba a taba lamunce shi ba, to ko shakka babu za ta soke hukuncin da kananan kotunan suka yanke.
Amma a fili wannan ba batun doka bane. Yaki ne na neman daukakar siyasa a Kano tsakanin Ganduje da Kwankwaso, inda Ganduje ke tutiya da kotuna a matsayin matakan makarkashiyar yi wa Kwankwaso zagon kasa.
Shawarata ga Shugaba Tinubu ita ce ya sa ido sosai domin wannan yanki ne na ha’incin gaske. Fushi na gaskiya game da rashin adalci a bayyane - a kan azabar da ke ci gaba da wanzuwa a cikin ƙasa – wanda ka iya haifar da tashin hankalin da ba za mu iya hasashen sakamakonsa ba.
An buga fassarar makalar nan a jaridar DILLALIYA ta ranar 29 ga Nuwamba, 2023.