Gwamnan Kano Ya Ƙaddamar Da Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 24 Domin Karfafa Ayyukan Al'umma Da Kuma Biyan Ƴan Fansho
- Katsina City News
- 21 Nov, 2023
- 577
A wani mataki na karfafa ababen more Rayuwa da kuma Magance matsalolin da suka shafi zamantakewar al’umma, Gwamnan Kano Abba Kabir-Yusuf ya Gabatar da ƙarin kasafin Kuɗi na Naira biliyan 24 ga Majalisar dokoki domin amincewa.
Kasafin kudin wanda ya hada da Naira biliyan 20 da kuma Naira biliyan 4 na kudin ma’aikata da kuma ƙara aiwatar da ayyukan da suka sa a Gaba da kuma inganta rayuwar mazauna Kano.
Gwamna Kabir-Yusuf, a jawabin da ya mika wa majalisar, Ya bayyana bukatar karin kasafin kudin, Inda ya danganta hakan ne sakamakon hasashen kuɗaɗen shigar da ake samu Daga ɓangarori daban-daban da suka haɗa da Kwamitin Kasafin Kudi na Tarayya (FAAC), Karin Haraji (VAT), Asusun Muhalli. Excess Crude Account (ECA), Excess Medium Term Loan (EMTL), Independent Power Projects (IPP) lamuni Daga Babban Bankin Najeriya (CBN), da kuma inganta kuɗaɗen shiga na cikin Gida (IGR).
Kasafin kudin da aka gabatar ya ba da fifiko ga ci gaban ababen more rayuwa, Ana sa ran wannan rabon zai ba da gudummawar ayyuka masu mahimmanci kamar gina tituna, inganta samar da ruwa, da fadada wuraren kiwon lafiya. Bugu da kari, kasafin kudin ya kebe kuɗaɗen ne domin biyan kuɗaɗen alawus-alawus ga ma’aikatan da suka yi ritaya, Tare da magance matsalar da ta dade tana jawo wa mutane da dama wahala.
KBC Hausa News