Harin 'Yan Bindiga a garin Danmusa: Majalisar Dokokin jihar Katsina ta koka
- Katsina City News
- 24 Oct, 2023
- 842
Majalisar Dokoki tayi Allah-wadai da harin da 'yan bindiga suka kai garin Ɗanmusa da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8 tare da yin garkuwa da mutane da dama a jihar Katsina.
Majalisar dokokin jihar Katsina tayi Allah-wadai tare da nuna alhini akan harin da yanbindiga suka kai a garin Ɗanmusa da yayi sanadiyar kashe mutane guda takwas.
Wannan ya biyo bayan wani kudiri na gaugawa da Ɗanmajalisa mai wakiltar karamar hukumar Danmusa Hon. Aminu A. Garba ya gabata a gaban zauren.
Katsina Post ta ruwaito to cewa daren ranar lahadi yanbindiga sun afka garin Ɗanmusa inda su ka bude wuta, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane guda takwas tare da yin garkuwa da mutane da dama.
Jim kaɗan bayan tattanawa akan ƙudirin, majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ta bukaci bangaren zartarwa da ya binciki al'amarin ya kuma ɗauki matakin da ya dace cikin gaggawa.
Sannan an gudanar da addu'o'i na musamman da niyyar Allah ya kawo mana karshen wannan matsaloli na tsaro da Jihar Katsina ke fama dasu.
Haka kuma Danmajalisa mai wakiltar karamar hukumar Danja Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai ya gabatar da kudirin tunatar da bangaren zartarwa kan gyaran azuzuwan makarantar firamare ta Jakara dake kofar kudu cikin garin Dabai dake cikin karamar hukumar Danja.
Shima Ɗanmajalisa mai wakiltar karamar hukumar Bakori Hon. Abdul Rahman Ahmed ya gabatar da ƙudirin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Bakori dake cikin karamar hukumar Bakori.
Bayan tattaunaw kan kudirorin da daukacin 'yan majalisar sukayi, daga karshe majalisar ta amince da kudirorin inda Kakakin majalisar ya umurci Akawun majalisar da ya tura ma bangaren zartarwa domin daukar matakin da ya dace.