FADA TSAKANIN SOJA DA FULANI YA HARGITSA GARIN DANMUSA... An tada cin kasuwar garin
- Katsina City News
- 22 Aug, 2023
- 1034
Muazu Hassan
@ katsina times
Wani fada da ya barke a kasuwar garin Danmusa a yau Talata, yayi sanadin kisan wasu fulani da kama wadansu tare da tayar da kasuwar garin dake ci yau Talata.
Wata Majiya mai karfi ta shaida mana Cewar wasu bakin sojoji ne suka zo suka kwana a sansani tsaro dake garin Danmusa.
Wadannan soja sune da safiyar yau Talata suka shiga kasuwa suna kamen Kan mai uwa da wabi ga duk wani bafullatani da suka gani.
Kamar yadda ganau a kasuwar suka tabbatar mana.
Wannan kame shi ya jawo fulanin dake kauyuka suka wo gangami suka nufo inda sojan ke tara yan uwansu da su da suka kama .
Wannan fito na fito ya aukar da musayar wuta tsakanin sojoji da fulanin.
Ganau ta tabbatar ma da jaridun mu cewa,sojojin sun fatattaki fulani sun kashe wasu sun kara kama wadansu.
Wannan fadan ya Sanya kasuwar garin ta Danmusa kowa yayi ta Kan shi.kuma mutanen garin suka fito kan tituna sukayi cirko cirko.
Munyi kokarin jin ta bakin sojoji amma sun ki daukar wayar da muka Kira.
Mun kuma Kira wayar shugaban karamar hukumar ta Dan musa da sakataren shi duk sun ki daukar
waya.
Ya zuwa rubuta rahoton nan garin na Danmusa ana cikin zaman dar dar.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
07043777779 08057777762