Daga wakilanmu @ www.katsinatimes.com
A Jihar Katsina, ’yan Majalisar Tarayya sun kasu kashi uku. Akwai ’yan majalisar da aka sake zaɓensu karo na biyu ko fiye, wato waɗanda suka koma kujerunsu bayan nasara a zaɓe. Akwai kuma sabbin ’yan majalisa da zuwansu na farko ke nan, waɗanda aka zaɓe su tun farkon zaɓen shekarar 2023.
Haka kuma akwai ’yan majalisar da kotu ta ba su kujeru bayan shari’a, inda wasu suka fara aiki da halartar zaman majalisa, amma daga bisani kotu ta ƙwace kujerunsu ta bai wa waɗanda suka yi nasara a shari’a.
Ayyukan ’yan majalisa sun kasu gida biyu: akwai ayyukan da doka ta ɗora musu, sannan akwai ayyukan da ake sa ran za su yi a matsayinsu na ’yan siyasa da wakilan al’umma.
A binciken da muka gudanar, mun gano wani ɗan Majalisar Tarayya da muka samu tabbacin cewa ba ya saɓa wa lokutan halartar zaman majalisar kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma yana yawan ziyartar al’ummar da suka zaɓe shi, yana zama da su ido da ido domin jin ƙorafe-ƙorafe da buƙatunsu kai tsaye.
Bugu da ƙari, ya kawo ayyukan raya ƙasa da dama a yankinsa, waɗanda suke nan a aikace.
Ya kuma ƙirƙiro shirye-shiryen bunƙasa al’umma, ciki har da bayar da tallafin kayan sana’a da jarin kasuwanci, horas da matasa, da samar musu da ayyukan yi a gwamnati da hukumomin tarayya.
Dangantakarsa da mazaɓarsa na cike yake da zaman lafiya, babu wata babbar matsala face ƙorafe-ƙorafen siyasa na yau da kullum, domin kamar yadda ake cewa, “mutum tara bai cika goma ba.” Wannan kuma shi ne zuwan sa na farko a Majalisar Tarayya.
Wannan ɗan majalisa shi ne Alhaji Aminu Balele, wanda aka fi sani da Ɗan Arewa, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kurfi da Dutsinma.
Ɗan majalisa na biyu ya shafe watanni kaɗan ne da zuwa Majalisar Tarayya, kasancewar kotu ce ta ba shi kujerar. Duk da haka, ya samu nasarar samar da manyan ayyuka kamar gina hanyoyi, gyaran asibitoci, samar da ayyukan yi, da bayar da tallafin kasuwanci da sana’o’i na ɗimbin kuɗaɗe.
Sai dai bincikenmu ya nuna cewa ba ya cikin manyan kwamitoci masu ƙarfi, kuma ba ya cikin na hannun daman Kakakin Majalisar Tarayya. Duk da haka, yana zaman lafiya da dattawa, matasa da ’yan siyasa a yankinsa, duk da cewa yankin na fama da manyan ƙalubale.
Wannan ɗan majalisa shi ne Alhaji Sani Aliyu Ɗanlami, mai wakiltar Katsina ta Tsakiya.
Akwai kuma wani ɗan majalisa mai tasiri a Majalisar Ƙasa, wanda ke iya fitar da jihar Katsina da ke tsomo wa jama'arsa kitse a wuta da fitar da su kunya wajen iya magana da bayyana ra’ayi. Sai dai yana fuskantar manyan ƙalubale a mazaɓarsa, duk da kasancewarsa tsohon ɗan majalisa. Sunansa Sada Soli Jibia, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Jibia da Kaita.
Haka kuma, wani ɗan majalisa daga shiyyar Daura, duk da ɗimbin ƙalubalen da yake fuskanta, har yanzu yana ƙoƙari. Wannan shi ne Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, mai wakiltar Mashi da Dutsi.
Akwai kuma wani ɗan majalisa daga yankin Daura wanda tauraron siyasarsa ta haska a baya, amma a yanzu ya fara dusashewa.
Yawancin ayyukan da muka bincika na tsofaffin ayyuka ne tun lokacin da yake kan ganiyarsa, duk da cewa ya kafa tarihi a baya.
Wasu ’yan majalisa a yankunan Funtua da Daura da muka bibiyi ayyukansu, mun lura cewa sun yi kama da na ɗan Majalisar Jiha ko Kansila, ba irin na Wakilin Majalisar Tarayya ba.
Wasu ayyukan kuma na wasu ’yan majalisa “flashing” ne kawai, har da wasu tallafin karatu da ake iƙirari, waɗanda idan aka yi bincike, za a gano cewa kuɗin da ɗalibi zai kashe kafin ya samu tallafin, kamar kuɗin mota da halartar taro, ya kai sama da kashi 60% na abin da za a ba shi.
A wasu lokuta, kuɗin da ake shelantawa a kafafen sada zumunta ba ya daidai da abin da aka kashe a zahiri.
Mun gano wani ɗan majalisa da ya bayyana adadin kuɗin da ya kashe a wata hidima, amma bincike ya nuna cewa bai wuce kashi 30% na abin da ya sanar ba.
Wasu ’yan majalisa kuma sun fi mayar da hankali kan ƙulla-ƙulla da shugabannin majalisa, maimakon aiki tuƙuru domin wakiltar al’ummarsu.
Wasu kuma, daga cikin ƙananan hukumomin da suke wakilta, guda ɗaya ce kawai ke cin moriya daga ayyukansu.
SANATOCIN JIHAR KATSINA
A ɓangaren sanatoci, bincikenmu ya nuna cewa Sanata guda ɗaya ne kawai ke yin abin da ya dace da jihar Katsina, kamar yadda doka da kuma tsammanin al’ummarsa suka tanada.
Wannan Sanata shi ne Muntari Ɗandutse, Sanatan da ke wakiltar yankin Funtua.
Sauran sanatocin kuwa, ƙorafe-ƙorafen da ake yi a kansu sun yi matuƙar shafar ayyukansu.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
All social media handles: katsina times
07043777779.08020570059