Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Ta Kori Dalibai 57 Saboda Laifin Yin Satar Jarabawa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02082025_111016_image1-757514.jpg

Katsina Times | Asabar, 2 ga Agusta, 2025

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina ta kori dalibai 57 saboda kama su da aikata laifin magudi a cikin jarabawa daban-daban.

Shugabar sashen yada labarai da hulɗa da jama’a ta jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan hukunci ya fito ne daga zama na 125 na majalisar jami’ar, bayan da kwamitin bincike kan magudin jarabawa na jami’a (UCEMC) ya gabatar da rahotonsa.

Binciken ya shafi sassan karatu daban-daban na jami’ar, kuma ya gabaci yanke hukuncin kora da ladabtar da daliban.

A cewar sanarwar, baya ga waɗanda aka kora, wasu dalibai biyar an dakatar da su daga karatu har zangon karatu biyu (2024/2025), tare da soke takardun jarabawarsu.

Haka kuma, an ba wasu biyu gargaɗi rubutacce, wanda zai kasance cikin kundin tarihin karatunsu na har abada.

Jami’ar ta UMYU ta bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na manufarta ta rashin lamunci ko sassaucin hukunci ga duk wani laifi na magudin jarabawa.

“UMYU za ta ci gaba da kare mutuncin tsarin karatunta, kuma ba za ta yi kasa a guiwa wajen ɗaukar matakin ladabtarwa a kan duk wani abu da zai kawo rashin gaskiya a jarabawarta ba,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ja kunnen dalibai da su kiyaye ƙa’idojin karatu tare da guje wa duk wani nau’i na magudi, domin kuwa za a ɗauki matakin da ya dace a gaba idan an sake kama laifi makamancin haka.

Follow Us