Minista Bosun Tijani Ya Kaddamar Da Tashar Masana’antar Dijital a Kano, Yayin da Gwamna Abba Ya Yaba da Tasirin Aikin

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03072025_134920_IMG-20250703-WA0121.jpg


Ministan Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Fasaha na Tarayya, Dr. Bosun Tijani, ya kaddamar da Tashar Masana’antar Fasaha (Digital Industrial Park – DIP) da ake sa ran za ta canza al’amuran tattalin arzikin fasaha tun daga tushe a jihar Kano.

Bikin kaddamarwar da aka gudanar a harabar tashar, ya nuna babbar nasara a kokarin Gwamnatin Tarayya na hada kan ‘yan Najeriya ta hanyar amfani da fasaha. Duk da cewa an kammala ginin wannan wuri tun a shekarar 2024, an yi masa mummunan barna a lokacin zanga-zangar kasa baki daya da ta faru a ranar 1 ga Agusta, 2024. Sai dai, da taimakon kamfanin IHS Towers, an gyara wurin gaba daya, kuma ya shirya fara aiki. 

A madadin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya isar da godiyar gwamnatin jihar ga Ministan bisa kishinsa da jajircewarsa ga Kano, da kuma hangen nesa wajen amfani da hadin gwiwar masu zaman kansu don cimma manyan ayyukan cigaba.

A wani bangare na nuna godiya da girmamawa, Mataimakin Gwamna, a madadin gwamnatin da al’ummar Kano, ya bai wa Dr. Tijani takobin gargajiya da hula, tare da bashi sarautar girmamawa ta Sarkin Yakin Digitalization, ma’ana Babban Jagoran Cigaban Fasahar Zamani, a matsayin yabo bisa rawar da ya taka wajen habaka ci gaban dijital a Kano da kasa baki daya.

Bikin kaddamarwar ya samu halartar wasu daga manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, jiga-jigan masana’antu, da wakilan kafafen yada labarai. Taron ya kara bayyana hadin gwiwar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatocin Jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu wajen bude damammaki a fannin fasaha a Najeriya.

Yanzu da Tashar Masana’antar fasaha ta fara aiki, ana sa ran karuwar ayyukan tattalin arzikin fasaha, samar da ayyukan yi, cibiyoyin kirkire-kirkire da shirye-shiryen gina kwarewa a fadin Jihar Kano da yankin Arewa gaba daya.

Follow Us