Daga Yusuf Kabiru.
Kamar yadda aka ga gabatar da Irin wannan taron a shekarar da ta wuce,haka a wannan shekarar ma karo na biyu ya gudana.
A ranar Asabar 25/5/2025 ne matasan ƙaramar Hukumar Roni da ke Jigawa masu ta'amulli da kafofin sada zumunta suka gudanar da taron ƙarawa juna sani da kyautata zumunci a tsakaninsu.
Matasan dai waɗanda suka fito daga garuruwa mabanbanta da na cikin gari da suke ƙaramar Hukumar Roni ɗin ne suka yi musharaka ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ba.
Shugaban Kwamitin taron Comrade Abba Muhammad ne ya yi bayanin maƙasudin taron da kuma waiwaye a kan nasarorin da aka samu a taron da aka gabatar na waccan shekarar.Hakan duk ya gudana bayan buɗe taron da addu'a da kuma taken ƙasar Nijeriya.
Yusuf Kabiru wani matashin ɗan Jarida mai sharhi a kan siyasar gabas ta tsakiya ne ya gabatar da muƙalarsa a kan " Social Media tsakanin amfani da cutarwa" Ɗan Jaridar ya nusar da mahalarta taron a kan wannan maudhu'i.Mai jawabi na biyu shi ne Matashin Malami Zubairu Nasiru Taƙwa in da ya gatabar da jawabinsa a kan "Ladubban amfani da Social Media a MAHANGAR addini" Bayan kammalarsa ne aka gabatar da mai jawabi na uku masanin harkokin kasuwanci a yanar gizo Shu'aibu Auwal Gwagwarwa Kano ne ya gabatar da ta sa muƙalar a kan "Yadda ake samun kuɗi da kasuwanci da Internet" Matashin masanin Internet ɗin ya bayyana yadda matasa za su yi amfani da wayar da ke hannunsu domin samarwa kan su kuɗaɗen shiga.Ya yi dogon bayani a kan illar ɓatawa kai lokaci wajen bibiyar ababen da ba za su amfanar da matasa ba.A yayin da ya amsa tambayoyin mahalartar a kan wannan maudhu'i.
Barrister Jamilu Salihu shi ne ya gabatar da muƙalarsa a kan "Dokokin amfani da Media da ƙaramar Hukumar Roni ta tanada a kan amfani da Social Media" Masanin shari'ar ya yi tilawar dokokin da kuma bayyana ababen da suke laifi da waɗanda ba laifi ba ne idan an aikata su.Daga bisa ya amsa tambayoyin mahalartar.
Taron dai ya haɗa da Shugaban 'yan Majalissar Jiha masu rinjaye Hon.Tambari Muhammad Ɗan Sure, tsohon ɗan Majalissar Jiha Alhaji Babangida, mataimakin Ciyaman na ƙaramar Hukumar Roni,wakilin DPO,Jami'in Hukumar farin kaya DSS,wakilin Hakimin Roni wanda Galadima Bala Muhammad ya wakilta,Limamin ƙaramar Hukumar Roni Malam Sabo Ya'u,Shugaban rukunin makarantar lafiya Alhaji Basiru Provost wanda Shaikh Mansur Ibrahim ya wakilta,da sauran ƙusoshin da suka halarci wannan taro mai albarka da ci gaba.
Alhaji Ibrahim babban masani ne sannan ɗan kishin garin Roni da tarbiyyar matasa ya sami halartar taron tattare da tunatar da matasa da ba su shawarwari a kan yadda za su gina kan su da amfani da Social Media domin haɓaka tattalin arziƙinsu.
Mahalarta kimanin 250 ne suka halarci wannan taron mai albarka.
Daga bisani an gabatar da Awards na girmamawa ga Mahalarta taron in da manyan baƙi suka karɓa cikin farin ciki.
Galadiman Roni Malam Bala Muhammad ne ya rufe taron da addu'a sannan a ka sallami al'umma.