Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon katunan cirar kuɗi ga waɗanda suka ci gajiyar shirye-shiryen tallafi na Bankin Duniya da ake kira 'Cash Transfer'.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Litinin a Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Tsafe.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin bai wa kowane mutum da ya cin gajiyar shirin tallafin kuɗi N75,000.00.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi.
“Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri.
“Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141.
“Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala, In Sha Allahu.
“Ga waɗanda suka ci gajiyar wannan shirin, ina tunatar da kuma gargaɗar ku da kada ku yi amfani da wannan kuɗi wajen biyan buƙatun cikin gida da aka saba yi, wannan ƙarfafawa ce da nufin ba ku damar saka hannun jari a nan gaba don tallafa wa kanku da iyalanku da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikinmu na gida da ma ƙasa baki ɗaya.
"Ina kira gare ku da ku yi amfani da wannan damar ta hanyar da ta dace, ku saka hannun jari a harkokin kasuwanci, kuma ku zama masu dogaro da kai."
Gwamnan ya gode wa Gwamnatin Tarayya, da abokan hulɗa, da masu ruwa da tsaki, musamman ma ofishin bayar da tallafin kuɗi na ƙasa, bisa jajircewa da bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin.
“Bari na yi amfani da wannan dama domin tabbatar muku da cewa gwamnatinmu za ta ci gaba da haɗa kai da kowane mutum ko ƙungiya domin ci gaban jiharmu.
"Da wannan nake farin cikin ƙaddamar da raba katunan cirar kuɗi don sauƙaƙe biyan kuɗin Cash Transfer ga waɗanda suka cancanta."