Ƙaramar Hukumar Funtua Na Maraba Da Wannan Sabon Tsarin Taimaka Wa Al'umma". Hon. Abdullahi Goya.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26042025_062848_FB_IMG_1745648831672.jpg

Daga: Muhammad Ali Hafizy @Katsina Times.

Shugaban karamar hukumar Funtua Hon. Abdullahi Goya ya yi maraba da tawagar sabon shirin taimaka wa mata musamman masu kananan jalli, (Najeriya For Women Project) karkashin jagorancin Hajiya Rabi Muhammad a yayin ziyarar da suka kai mashi a ofishin shi ranar Juma'a 25 ga watan Afrilu na shekarar 2025.

Hajiya Rabi Muhammad, wadda take jagorantar shirin ta bayyana ma shugaban karamar hukumar, irin yadda tsarin taimakon zai kasance da kuma da kuma abubuwan da aka bukata daga gare su na mutanen da zasu yi aikin da sauran abubuwan da suka shafi aiki.

Shugaban karamar hukumar ya nuna matukar jin daɗin shi ga me da wannan sabon shirin da za'a gabatar, sannan ya yi godiya ga Allah da ya sanya aka zabi karamar hukumar shi a matsayin kananan hukumomin da za'a fara wannnan shirin da su.

Haka zalika tawwagar ta zarce zuwa gidan Sarkin Maskan Katsina, Hakimin Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, domin sanar da su sabon shirin a matsayin shi na shugaban al'umma, tare da bayyana nashi yadda shirin zai kasance.

Ya yi na'am da shirin tare da yin fatan alkairi ga wadanda zasu gudanar da shirin, da ma sauran wadanda zasu amfana da shirin.

Follow Us