Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Katsina ya kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa ta (Public-Private Partnership – PPP) da Kamfanin Sahel Medicare Services Limited domin yin aiki tare a fannin ayyukan dakin gwaje-gwaje, bisa sabbin umarnin gwamnatin tarayya.
A yayin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaban tawagar Sahel Medicare Limited, Malam Nasir Muhammad Abdulbaki, ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka matuƙa wajen rage matsalolin da ke fuskantar fannin lafiya tare da ƙarfafa aiki da ƙara inganci.
Malam Nasir ya bayyana yakinin cewa wannan mataki zai kawo sauyi mai ma’ana da cigaba a harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.
Ya kara da cewa yarjejeniyar za ta gudana na tsawon shekaru hudu, inda ake sa ran Sahel Medicare Limited za ta tallafawa ayyukan asibitin FTH bangaren dakin gwaje-gwaje.
Malam Nasir ya tabbatar da cewa Sahel Medicare za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantattun ayyukan gwaje-gwaje tare da FTH a tsawon lokacin yarjejeniyar.
Ya kuma jaddada cewa Sahel Medicare Limited na da kwarewa mai yawa, inda ya bayyana cewa kamfanin ya riga ya yi nasarar yin aiki tare da hukumomin gwamnati da kungiyoyin masu zaman kansu a fadin ƙasar nan a fannin lafiya.
Malam Nasir ya sake tabbatar da kudirin Sahel na ci gaba da riƙe matsayinta a matsayin jagorar cibiyar kiwon lafiya mai zaman kanta a Najeriya.
Daga nan ya nuna godiyarsa ga hukumar asibitin FTH bisa hadin kai, goyon baya da sadaukarwa da suka nuna tun daga farkon tattaunawa har zuwa cimma yarjejeniyar PPP a hukumance.