Mai Ba Gwamnan Katsina Shawara Kan Harkokin Matasa Ya Nemi Afuwa Kan Kalamansa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06032025_163223_IMG-20250306-WA0077.jpg

Katsina Times 

Mai ba Gwamnan Katsina shawara kan harkokin matasa, Alhaji Abubakar Tsanni, ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi na rashin goyon bayan 'yar takarar kungiyar matasa ta NYCN, Hadiza Saulawa.

Tsanni ya bayyana hakan ne yayin taron bayar da takardar shaida ga kungiyoyin matasa da za su shiga zaben NYCN. Taron, wanda Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Katsina, Alhaji Aliyu Lawal Shargalle, ya jagoranta, ya gudana cikin nishadi da fahimtar juna.

A nata bangaren, Hadiza Saulawa ta ce ta yafe masa kuma ta dauki lamarin a matsayin wani darasi a siyasa. Ta bayyana wa jaridar Katsina Times cewa hakan ya kara fito da kwarjininta tare da mutunta gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda.

Hadiza Saulawa ta kara da cewa, idan Allah Ya ba ta nasara a wannan kujera, za ta hada kai da gwamnatin jihar, ta tarayya, da kungiyoyin kasa da kasa domin inganta rayuwar matasan Katsina.

Ta kuma jinjina wa dattaku da hangen nesa na Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda

Follow Us