Ba a ga Buhari da El-Rufai da Amaechi ba a taron kwamitin ƙoli na APC

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26022025_175156_FB_IMG_1740592094544.jpg


Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun hallara a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja don taron kwamitin ƙoli na ƙasa (NEC).

Duk hanyoyin da ke zuwa wurin taron a titin Blantyre an killace su ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro masu dauke da makamai, ciki har da sojoji.

An takaita zirga-zirgar motoci da mutane a titin Blantyre, sannan an hana ‘yan jarida shiga duk da cewa kakakin jam’iyyar, Felix Morka, ya fitar da jerin sunayen ‘yan jarida da aka tantance da safe a ranar Laraba.

Daga cikin wadanda suka isa wurin taron da wuri sun hada da dukkan  shugabannin jam'iyyar na kasa (NWC), shugabannin jam’iyya na jihohi, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, Ministan Kasafi da Tsare-Tsare na Kasa, Atiku Bagudu, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.

Gwamnonin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Neja, Legas, Kogi, Ogun, Imo, mataimakin gwamnan Ebonyi, da tsofaffin gwamnonin Kogi, Kebbi, Neja, Zamfara, da Filato sun halarta.

Daga cikin wadanda ba su halarci taron NEC ba sun hada da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, da tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Shugaban jam’iyyar, Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Goodwill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas sun isa wurin taron da misalin karfe 12 na rana. Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, ne ya jagoranci taron.

Wannan shi ne taron NEC na farko tun bayan hawar Tinubu mulki a watan Mayun 2023, kuma ya biyo bayan taron majalisar kolin jam’iyyar da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa a Abuja.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da El-Rufai da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Salihu Lukman, sun koka kan rashin dimokuradiyya a cikin jam’iyyar mai mulki.

Follow Us