Wasu da ake zargin masu garkuwa da Mutane ne sun yi sace wata mata mai shekaru 60, Talatu Ali, daga Asibitin masu larurar kwakwalwa da ke Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da take jiran ganawa da likita.
Daily Trust ta rawaito cewar masani kan yaki da ta'addanci, Zagazola Makama, ɗan uwanta Nasiru Aliyu tare da wani ɗan uwanta, Aliyu Garba, ne suka kawo ta asibitin a ranar 19 ga Fabrairu, 2025.
Amma yayin da suke layin jiran ganawa da likita, sai suka lura cewa ba su iya gano inda take ba.
Duk ƙoƙarin da aka yi don gano ta a cikin harabar asibitin ya ci tura, lamarin da ya sa iyalanta suka kai rahoto ofishin 'yansanda na Dawanau.
Sai dai, a ranar 21 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:00 na safe, Aliyu ya samu kiran waya daga wani lamba da ba a sani ba inda aka tabbatar masa cewa matar tana hannunsu.
Rundunar 'yansandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ko da yake yankin Arewa maso Yamma na fama da matsalolin 'yan fashi da garkuwa da mutane, Kano ta kasance cikin yanayi na zaman lafiya a mafi yawan lokaci.
Daily Nigeria Hausa