Muhammad Ali Hafiziy, Katsina Times
A ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu 2025, an gudanar da bikin ƙaddamar da sabbin shugabannin kasuwar Himata da aka fi sani da "Chake" a birnin Katsina. Taron ya gudana ne a bakin shiga kasuwar, da ke kan titin Kofar Guga, inda aka kuma buɗe asusun kungiyar 'yan kasuwar domin ƙarfafa harkokin kasuwanci.
Bikin ya samu halartar fitattun ‘yan kasuwa da manyan baki, ciki har da Hon. Ali Abu Albaba, Alhaji Musa Almusik, Alhaji Lolo Dakare, Alhaji Hamza Makafia, Alhaji Audun Malam, da zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isa Miqdad. Haka kuma, ƙananan ‘yan kasuwa da sauran al'ummar gari sun halarta domin shaida wannan muhimmin biki.
A jawabansu, Hon. Ali Abu Albaba da Hon. Isa Miqdad sun yabawa tsofaffin shugabannin kasuwar bisa ƙoƙarin da suka yi na habaka kasuwar zuwa wannan mataki da take a halin yanzu. Sun kuma bukaci sabbin shugabanni da su ɗauki ragamar kasuwar da cikakken azama, tare da tabbatar da tsare gaskiya da adalci wajen tafiyar da harkokin kasuwanci.
Haka nan, Alhaji Lolo Dakare ya jinjinawa shugabannin kasuwar, musamman dattawan yankin da manyan ‘yan kasuwa da suka taka rawa wajen cigaban kasuwar. Ya kuma shawarci sabbin shugabanni su yi aiki tukuru domin tabbatar da ci gaban ‘yan kasuwa da kuma samar da tsari mai kyau ga matasa.
A nasa jawabin, sabon shugaban kasuwar, Alhaji Saminu Aliyu, ya godewa mahalarta taron da kuma ‘yan kasuwa baki daya bisa goyon bayan da suka ba shi. Ya tabbatar da cewa zai yi shugabancinsa bisa gaskiya da rikon amana, tare da yin aiki don ci gaban kasuwar ba tare da wata matsala ba.
Wannan rantsuwa na sabbin shugabanni na nuni da sabuwar tafiya ga kasuwar Himata, inda ake sa ran ci gaba da inganta harkokin kasuwanci tare da ƙara haɗin kai a tsakanin 'yan kasuwa da al'umma gaba ɗaya.