Dokar haraji itace hanya mafi inganci wajen samarwa Nijeriya arziki mai ɗorewa - Tinubu
- Katsina City News
- 17 Dec, 2024
- 220
Shugaba Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi wani muhimmin mataki ne na gina arzikin kasa mai dorewa da wadata ga daukacin 'yan Najeriya.
Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na kasa ne ya gabatar da jawabin shugaban kasa a ranar Lahadi a bikin karramawar yabo na 2024 na 'Nigerian Media Merit', wanda aka gudanar a Cibiyar Muson da ke Legas.
Tinubu ya ce duk da cewa ra'ayi na iya bambanta dangane da cikakkun bayanai na sake fasalin harajin da ake son yi alal misali, akwai matsayar kasa kan bukatar sake yin garambawul ga tsarin haraji na yanzu.
Ya ce ya yi imanin cewa gwamnatin sa na Kawo manufofi a tsare kuma cikin nazari mai zurfi da nufin samar da sakamako mai ɗorewa.
S cewar Tinubu, gwamnatin sa na kan hanyar maido da Najeriya bisa turbar da ke bukatar cikakken tsarin da zai magance sauye-sauyen tattalin arziki, bunkasa tattalin arzikin al'umma, samar da ababen more rayuwa, samar da arziki, da kuma ci gaba.
"Daga cikin manyan gyare-gyaren da muka yi akwai wanda aka mayar da hankali kan haraji, wanda ya zuwa yanzu daya daga cikin manyan matakan da suka dace don dora Najeriya kan turbar dorewar dukiyar kasa da wadata ga daukacin al’ummarmu," in ji shi.
Culled from Daily Nigeria Hausa