YANDA AKE DINKIN TAMBARI
- Katsina City News
- 04 Dec, 2024
- 639
Da farko ana samun iccen ƙokon da ake amfani da shi, sai a samu fatar Bujamin sa riƙaƙƙe mai fata mai kyau, a wancan lokacin ana amfani daTsamiya a jemeta, saɓanin yanzu ba'a yin haka, haka nan ake saka fatar sai daga baya asa sanfefe ko ɗan ƙaramin Dutse a cire gashin.
Bayan an gama jemeta sai a yanyankata dai-dai girman bakin kofar ƙokon tambarin, sai ayi mashi rawani da jijiyar Raƙumi, saɓanin na yanzu da igiyar kaba ake yin shi.
A ƙasan tambarin akwai wani abu da ake cema zobe, idan aka yi masa rawani sai ayi amfani da fatan wajen ɗauri, wadda za'a zurata daga saman rawanin ta biyo ta zoben, za'ayi kamar zagaye biyar ko shida.
Bayan an gama, sai asamu matasa majiya ƙarfi, su ja fatar ja bana wasa ba, idan ya janyu sai akuma teɗeshi.
Taɗewar ita ce, za'a sa fatar tsakiyar ƙoƙon tambarin tsakanin fatocin, sai nan ma a sake jansu su yi Dama da Hagu.
Wanann aiki yana buƙatar kayan aiki, kamar wuƙa, ƙaho, filaya, Makuli busasshiyar fata da sauransu.