Katsina: Ma'aikata Za Su Fara Cin Gaskiyar Sabon Albashi A Watan Disamba Mai Kamawa
- Sulaiman Umar
- 30 Nov, 2024
- 227
Daga Sulaiman Ciroma
A daren jiya juma'a ne gwamnatin jihar Katsina ta sanarwa manemai labarai cewa ma'aikatan jihar na karamar hukumar Katsina da sauran kananan hukumomi 35 za su fara cin gaskiyar sabon karancin albashi na Naira N70,000 a karshen watan Disamba mai kamawa.
Sanarwar ta fito ne karkashin kwamitin da mai girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya kafa don tattauna batun karancin albashi tare da samun matsaya.
Kwamitin wanda mai girma sakataren gwamnatin Alhaji Abdullahi Garba Faskari ke jagoranta tare da sauran masu ruwa da tsaki da kungiyar kwadago reshen jihar Katsina sun yi hadin gwiwa don tattauna batun sabon albashin inda suka samu matsaya akan za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin a watan Disamba mai kamawa.